Shugaba Bola Tinubu Ya Bar Legas Zuwa Abuja Bayan Kammala Hutun Sallah

Shugaba Bola Tinubu Ya Bar Legas Zuwa Abuja Bayan Kammala Hutun Sallah

  • Shugaba Bola Tinubu ya koma Abuja domin ci gaba da gudanar da ayyukansa na shugaban ƙasa bayan ya shafe kwanaki huɗu yana hutu a Legas
  • Tinubu ya isa birnin Legas ne a ranar Talatar da ta gabata gabanin bikin babbar sallah, inda ya gana da wasu sarakunan gargajiya na yankin Kudu maso Yamma
  • A baya dai shugaban ya je birnin Landan, inda rahotanni suka ce ya yi ganawar sirri da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ikeja, Lagos - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bar birnin Legas a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuli, zuwa Abuja, bayan shafe kwanaki 4 yana hutun babbar sallar Idi a can.

An hangi shugaban tare da rakiyar jami'an tsaro sun shiga jirgi a wani ɗan gajeren faifan bidiyo da NTA ta wallafa a shafinta na Tuwita.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Tinubu na wata muhimmiyar ganawa da Shugaba Umaro Embalo na Guinea Bissau

Shugaba Tinubu ya koma Abuja
Tinubu ya bar Legas zuwa Abuja. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Yadda Shugaba Tinubu ya gabatar da hutunsa na Sallar Eid-el-Kabir

A ranar jajiberin sallah, wato ranar Talata 27 ga watan Yuni ne dai Shugaba Bola Tinubu ya taso daga birnin Landan na ƙasar Birtaniya zuwa Legas.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban ya baro Landan ɗin ne bayan halartar taron ƙoli na hada-hadar kuɗi na duniya a birnin Paris dake ƙasar Faransa, a ranar Laraba 21 ga watan Yuni.

Bayanai sun nuna cewa Shugaba Tinubu zai koma bakin aiki ne a ranar Litinin, 3 ga watan Yuli a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

A zuwansa Turai domin halartar taron na kwanaki biyu, Shugaba Tinubu da farko ya shirya dawowa Najeriya ranar Asabar 24 ga watan Yuni.

Yadda Shugaba Tinubu ya tashi daga Paris zuwa Landan

Bayan fasa dawowarsa gida Najeriya ranar Asabar, fadar shugaban ƙasa ta sanar da sauya akalar tafiyar Tinubu, inda ta ce ya tafi zuwa Landan daga birnin Paris a wata ziyarar sirri.

Kara karanta wannan

Ko Sama Ko Kasa: An Nemi Mataimakin Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Na Kasa An Rasa

A ziyarar da Tinubu ya kai birnin Landan, ya yi wata ganawar sirri da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, inda har aka yi zargin cewa har ya nemi a daina binciken mambobin majalisarsa.

Sai dai kuma tsohon mai magana da yawun tsohon shugaban ƙasar, Garba Shehu ya karyata wannan ikirari, inda ya ƙara da cewa babu wanda ya san abinda su biyun suka tattauna.

Kalli bidiyon a kasa:

An buƙaci Tinubu ya ƙyale Wike, ya naɗa wani daban matsayin minista daga Ribas

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoton cewa wasu dattawan jihar Ribas sun buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Sanata Magnus Abe matsayin minista daga jihar.

Dattawan sun koka cewa ana neman a jingine Magnus Abe a gefe cikin majalisar zartaswar gwamnatin Tinubu da ake shirin ƙaddamarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng