Peter Obi Ya Goge Rubutun Da Ya Yi Yana Mai Kiran Tinubu Da Shugaban Kasa
- Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), ya sake shiga wata takaddama
- Rahotanni sun tabbatar da cewar a karon farko, Peter Obi ya kira Bola Ahmed Tinubu da sunan shugaban kasar Najeriya a wata wallafa da ya yi a Twitter
- Sai dai kuma, daga bisani an tabbatar da cewar ya goge rubutun sannan ya maye gurbinsa da wani inda ya ki kiran Tinubu da shugaban kasa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya goge wallafar da ya yi a twitter inda ya kira Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da "mai girma shugaban kasa."
Kamar yadda jaridar Guardian ta rahoto, Obi ya goge wallafar da ya yi a twitter yana mai caccakar ayarin motoci 120 na shugaban kasa Tinubu lokacin da ya isa jihar Lagas bayan ya dawo daga tafiyar da ya yi zuwa kasar waje.
Ya rubuta:
"...da ke nuna mai girma shugaban kasa tare da ayarin motoci kimanin guda 120. Yayin da ban samu damar ganin bidiyon ba, shawarata na nan tsayin daka, cewa ya zama dole sadaukarwa don inganta Najeriya ya fara daga kan shugabanni a dukkan matakai na gwamnati..."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yan awanni bayan ya yi rubutun a Twitter, sai Obi ya goge shi sannan ya maye gurbinsa da wani rubutun inda ya ki kiran Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya.
Wallafar Obi yana caccakar Tinubu
Rubutun da aka maye gurbin wancan da shi na cewa:
"Ba zai yiwu mu ci gaba da yi wa mutanen wa'azin sadaukarwa ba tare da muma mun sadaukar ba.
"Ya zama dole sadaukarwar ya fara yanzu daga kan shugabanni a gani, kuma a dunga aunawa a kodayaushe saboda mutane na shan wahala. Ya zama dole mu kasance a sahun gaba wajen magance wahalhalu.”
Har yanzu Peter Obi na a kotun zabe yana kalubalantar nasarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa da ya gabata.
Tinubu ya bayyana abun da ya sa wani sojan ruwa ya sharara masa mari a Amurka
A wani labari na daban, shugaban kasa Bola Tinubu ya tuna yadda ya yi rayuwa a matsayin direban tasi a kasar Amurka lokacin da yake matashin saurayi.
Tinubu ya bayyana cewa ya taba daukar wani sojan ruwa a tasi dinsa inda ya caje shi kudi da ya zarta kima bisa kuskure wanda hakan ya sa sojan sharara masa mari.
Asali: Legit.ng