Ortom Ya Musanta Rahoton Cewa Shugaba Tinubu Ya Nada Shi a Matsayin Minista
- Samuel Ortom ya musanta rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa shugaba Tinubu zai naɗa shi a matsayin Minista
- Rahoton wanda ya karaɗe soshiyal midiya ranar Alhamis ya yi ikirarin cewa Ortom ya shiga jerin Ministocin da Tinubu zai naɗa
- Sai dai a wata sanarwa, Ortom ya karyata labarin kana ya roƙi 'yan Najeriya da su yi watsi da shi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Benue - Tsohon gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya musanta rahoton da ke yawo a soshiyal midiya cewa gwamnatin Bola Tinubu ta zaɓe shi cikin waɗanda zata naɗa Ministoci.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa jihar Benuwai ta ɓarke da murna ranar Alhamis, bayan jita-jita ta karaɗe kafafen sada zumunta cewa tsohon gwamnan ya shiga cikin mutanen da zasu dafe muƙami.
Bisa haka mutane da dama kama daga abokan siyasa da magoya bayan Samuel Ortom sun ɓarke da murna tare da taya tsohon gwamnan murnar samun muƙami.
Menene gaskiyar rahoton da ke yawo?
Amma a wata sanarwa da Ortom ya fitar ranar Jumu'a a Makurdi, babban birnin Benuwai ta hannun mai magana da yawunsa, Terver Akase, ya musanta jita-jitar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mista Ortom, ɗaya daga cikin gwamnonin G5 da suka yaƙi Atiku Abubakar a inuwar PDP, ya ayyana rahoton da kagaggen labari, wanda ba shi da madogara.
Daily Post ta rahoto wani sashin sanarwan ya ce:
"An jawo hankalin tsohon gwamnan jihar Benuwai da ya gabata, Samuel Ortom, kan wani rahoto da yake yawo a kafafen sada zumunta cewa an zaɓe shi cikin waɗanda za'a ba Minista."
"Muna rokon ɗaukacin al'umma su yi fatali da rahoton baki ɗayansa domin ba komai bane illa ƙarya da kuma ɓata. Ortom ya yaba wa waɗanda suka kira waya domin tabbatar da labarin."
A ranar 29 ga watan Yuni, 2023, Samuel Ortom, ya sauka ya miƙa wa jam'iyyar APC mulkin jihar Benuwai bayan nasarar da ta samu a babban zaɓen 2023.
Fada da Cikawa: Gwamna Aliyu Ya Fara Rabawa Nakasassu N6,500 Duk Wata
A wani labarin na daban kuma Gwamnan Sakkwato Ahmad Aliyu ya cika alƙawarin da ya ɗauka na dawo wa tallafin da ake baiwa naƙasassu kowane wata.
Rahoto ya nuna cewa naƙasassun sun cika manyan cibiyoyin rabon kuɗin a kananan hukumomin Sakkwato ta arewa , Dange Shuni da Gwadabawa.
Asali: Legit.ng