Kungiya Ta Yi Tir Da Rahoton Da Ke Sukar Yadda Gwamna Sani Ke Tafiyar Da Harkar Tsaron Kaduna
- Kungiyar masu kare Gaskiya da Adalci (Truth and Justice Defenders Forum) reshen jihar Kaduna ta yi Allah wadai da wani rahoto da aka fitar kan gwamnan Kaduna
- Rahoton ya zargi gwamnan Kaduna, Uba Sani da nuna bambanci wajen tafiyar da harkokin tsaro a jihar
- Kungiyar ta ce wasu 'yan siyasar jihar ne ke daukar nauyin irin wadannan rahotanni da nufin kara rikita jihar
Kaduna - Kungiyar masu kare Gaskiya da Adalci (Truth and Justice Defenders Forum) reshen jihar Kaduna, ta yi martani kan wani rahoto da wata kafar yada labarai ta wallafa.
Rahoton ya nuna shakku kan yadda Gwamna Uba Sani ke gudanar da harkokin tsaro a jihar Kaduna, wanda kungiyar ta yi zargin cewa an biya su ne su yi hakan.

Source: Twitter
Wata kafar yada labarai ta zargi Uba Sani da nuna bambanci

Kara karanta wannan
Kano: NLC Za Ta Shiga Takun Saka Da Abba Gida Gida Kan Albashin Ma’aikata Fiye Da 10,000
Wata kafar yada labarai ta zargi Gwamna Uba Sani da yin watsi da wasu sassa na jihar da yan ta'adda ke adaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kazalika, kafar ta zargi tsohon Gwamna Nasir El-Rufai da yin katsalandan a cikin harkokin jihar ta hanyar bai wa gwamna mai ci shawarwari kan yadda zai tafiyar da lamuran jihar.
Rahoton ya kuma zargi Gwamna Uba Sani da rashin nuna damuwa kan harkar tsaro a jihar ta hanyar tafiya aikin Hajji a kasar Saudiyya.
A martanin da kungiyar ta mayar, ta bayyana rahoton a matsayin murdadde, wanda aka nuna rashin kwarewa, kuma mara tushe da wani dan siyasar jihar da ya rasa kimarsa ya dauki nauyi, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Shugaban kungiyar ya yi barazanar bayyana sunayen masu daukar nauyin irin rahoton
Shugaban kungiyar Sabo Abbah Anas, a cikin wata sanarwa cikin kakkausar murya ya ce, suna da masaniya kan ainihin mai daukar nauyin irin wadannan munanan labarai da nufin kara tada zaune tsaye a jihar.

Kara karanta wannan
“Bana Biyan Kudin Haya”: Budurwa Ta Baje Kolin Gidanta Na N250m, Komai Ya Ji a Gidan
Ya kara da cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen bayyana sunayen wadanda ke daukar nauyin labaran muddun suka ci gaba.
Anas ya shawarci 'yan siyasar jihar, musamman wani da ya kira da 'marubuci mai neman suna' a yanar gizo, da su guji yin kalaman da ba na gaskiya ba kan tsaro a jihar.
A kalamansa:
"Mun lura da cewa, wani sashe na kafafen yada labarai ba su yin taka-tsan-tsan wajen bayar da rahotannin halin da ake ciki a bangaren tsaro a jihar Kaduna, wanda hakan ke kara ta'azzara matsalar tsaron."
“Duk da irin wannan sanannen son zuciya na wannan kafafen yada labaran, gwamnatin jihar ba ta taba yin yin Allah wadai da su ba a duk lokacin da suka yi abubuwan da suka karya ka'ida.”
“Muna sa ran mamallakan wadannan kafofin yada labaran za su gyara ayyukansu, tare da bin duk ka’idojin aiki game da yada labarai da bayar da rahoto."
A cewar kungiyar, abin mamaki ne a ce an kebance iya jihar Kaduna kadai wajen bayar da irin wannan rahoto kan hare-haren 'yan ta'addan, kamar yadda Blueprint ta wallafa.

Kara karanta wannan
Cire Tallafi: Jam'iyyar PDP Ta Yabi Tinubu Kan Matakan Da Ya Ke Dauka, Ta Ce Ya Yi Bajinta
Ta bayyana cewa matsalar tsaron ta fi kamari a sauran jihohin Arewa irinsu Zamfara, Katsina, da Neja fiye da yadda yake a jihar Kaduna.
Gwamna Uba Sani: Gwamnonin Arewa Maso Yamma Ba Za Su Sake Sulhu Da Yan Bindiga Ba
A wani rahoton kun ji cewa Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya ce shi da sauran takwarorinsa na jihohin Arewa maso Yamma ba za su yi sulhu da yan bindiga ba.
Sani ya ce sun yanke wannan shawarar ne bayan wani taro na musamman da suka yi inda aka tattauna hanyoyin da za a bi don kawo karshen kallubalen tsaro a yankin.
Asali: Legit.ng