Kwankwaso Bai Fada Mana Komai Ba Kan Maganar Komawa APC, Buba Galadima

Kwankwaso Bai Fada Mana Komai Ba Kan Maganar Komawa APC, Buba Galadima

  • Dattijo kuma jigon jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya ce babu abin da Kwankwaso ya ce musu game da komawarsa APC
  • Galadima ya bayyana haka ne yayin hirarsa da 'yan jaridu a ranar Alhamis 29 ga watan Yuni a Abuja babban birnin Tarayya
  • Ya ce dan takarar jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso ya shirya yin aiki tare da Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu

FCT, Abuja - Jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso bai ce musu komai ba game da komawarsa APC.

Galadima ya bayyana haka ne yayin hirarsa da 'yan jaridu a ranar Alhamis 29 ga watan Yuni a Abuja.

Buba Galadima ya ce Kwankwaso bai ce musu komai ba kan komawarsa APC
Jigon Jam'iyyar NNPP, Buba Galadima. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Jigon jam'iyyar NNPP, ya ce Kwankwaso ya shirya don yin aiki tare da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare, Sanata Ya Faɗi Mutum 2 Tal da Suka Jawo Atiku Ya Sha Kashi Hannun Tinubu a Zaɓen 2023

Galadima ya ce basu san komai ba kan komawar Kwankwaso APC

A cewarsa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Kwankwaso bai fadawa kowa cewa zai sauya sheka zuwa jam'iyyar APC ba, mutane ne kawai suke magana.
"Abin da muka sani shi ne wanda ya yi nasara shi ne da komai, idan Tinubu yana so ya yi gwamnatin hadaka, wannan ba laifi ba ne."

Idan ba a mantaba, Rabiu Kwankwaso ya gana da shugaban kasa, Bola Tinubu a Abuja ba sau daya ba bayan zaben gama gari a watan Faburairu.

Ana rade-radin Tinubu zai ba wa Kwankwaso mukamin siyasa

Bayan ganawar tasu, akwai jita-jita da ke yawo cewa Kwankwaso na iya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki, Daily Post ta tattaro.

Har ila yau, ana tunanin Tinubu zai iya yiwa Kwankwaso tayin mukamin siyasa a gwamnatinsa, wanda hakan ke shirin kawo matsala tsakanin Tinubu da tsohon gwamnan Kano, Umar Ganduje, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Badakalar Takardar Makarantar Tinubu: Omokri Ya Bayyana Abun da Ya Bankado a Jami’ar Chicago, Ya Wallafa Wasika

Buba Galadima har ila yau, ya shawarci 'yan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da na Labour, Peter Obi da su bar asarar kudinsu wurin kalubalantar zaben da aka gudanar.

Jigon NNPP Ya Yabi Tinubu, Ya Hango Alheri Ga 'Yan Najeriya

A wani labarin, jigon jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya bayyana cewa matakan da Tinubu ya ke dauka suna kan hanya.

Ya ce a matsayinsa na dan jam'iyyar APC ya dauko hanyar gyara kasar Najeriya inda ya yi fatan dorewar hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.