Shugaban INEC Ya Fi Gwamnan CBN Yi Wa 'Yan Najeriya Illa, Bula Galadima
- Buba Galadima ya yi kira ga shugaban kasa Tinubu ya kori Farfesa Mahmud Yakubu daga mukamin shugaban INEC
- Jigon NNPP kuma tsohon makusancin Buhari ya ce abinda Yakubu ya aikata ya fi illa fiye da laifin Godwin Emefiele
- INEC karkashin Mahmud Yakubu na shan suka biyo bayan gaza dora sakamakon zaben shugaban kasa a Intanet
Babban jigon jam'iyya mai kayan daɗi NNPP, Buba Galadima, ya yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kori shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta, Farfesa Mahmud Yakubu.
Galadima ya yi wannan kira ne yayin hira da gidan talabijin Channels tv a cikin shirinsu mai suna, "Political Paradigm."
Jigon siyasar kuma tsohon makusancin Muhammadu Buhari ya zargi shugaban INEC da sauya muradin 'yan Najeriya a lokacin zaɓen shugaban ƙasan da ya gabata a 2023.
Ya ce abinda Farfesa Yakubu ya aikata, ya zarce laifukan da dakataccen gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya yi wa 'yan Najeriya muni, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kalamansa ya ce:
"Dole shugaban INEC ya sauka, abinda ya aikata ya fi na Emefiele muni. Ya haɗa baki da wasu tsirarun mutane sun juya muradin 'yan Najeriya. Ya aikata babban laifin da ya fi na kowa."
Yadda yan Najeriya suka dawo daga rakiyar INEC
Hukumar zaɓe INEC karkashin jagorancin Farfesa Mahmud Yakubu, na shan suka daga mutane daban-daban bisa gazawarta wajen dora sakamakon zaɓe a Intanet.
Sai dai duk da caccakar da INEC ke sha kan wannan ci gaban, hukumar ta kare kanta da cewa hakan ta faru ne sakamakon 'yar tangarɗar da aka samu a lokacin zaɓen.
Haka zalika masu sa ido kan zaɓe na ƙunguyar tarayyar Turai sun bayyana cewa yardar da al'umma suka yi wa INEC ta lalace sakamakon abinda ya faru.
Amma yayin martani, INEC ta ce tangarɗar da aka samu wajen ɗora sakamakon zaɓen shugaban kasa a intanet ranar 25 ga watan Fabrairu, bai kai ya lalata zaɓen da aka gudanar a ƙasa baki ɗaya ba.
"Ku Ji Tsoron Allah" Malamai Sun Aike da Sako Ga Shugabannin Siyasa
A wani rahoton kuma Malamai sun roki shugabannin siyasa da suka hau madafun iko su ji tsoron Allah yayin sauke nauyin jama'a da Allah ya ɗora musu.
A cewar malaman ya kamata 'yan Najeriya su kwankwaɗi romon ayyuka da tsarukan da zasu tsamo su daga talauci sakamakon sadaukarwan da suka yi.
Asali: Legit.ng