Sanatoci 3 Su na Tseren Rike Mukami Mafi Tsoka Bayan Shugaba a Majalisar Dattawa

Sanatoci 3 Su na Tseren Rike Mukami Mafi Tsoka Bayan Shugaba a Majalisar Dattawa

  • An fara tsere a kan wanda zai dare kan kujerar shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa a Najeriya
  • Ali Ndume zai so ya sake samun wannan matsayi ganin shi ne Shugaban yakin neman zaben Akpabio
  • Opeyemi Bamidele da Fatai Buhari sun dogara da cewa Kudu maso yamma ya dace a kai kujerar

Abuja - Bisa dukkan alamu za a gwabza tsakanin Sanatocin kasar nan wajen zaben wanda zai zama sabon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa.

Vanguard ta ce wasu Sanatoci daga yankin Arewacin Najeriya su na harin wannan mukami, amma kuma akwai masu ganin ba haka abin ya kamata ba.

Akwai Sanatocin kudu maso yamma da su ke ganin tun da shugaban kasa daga yankinsu ya fito, a al’adar majalisa, su za a ba kujerar jagora daga APC.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Kirkiro Sabuwar Hanyar Tatsar Kudi Daga Masu Hawa Titi

Majalisar Dattawa
Zaman Majalisar Dattawa Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Masu ra’ayi akasin haka su na la’akari da cewa tun da Abdulaziz Yari bai yi nasara a zabe ba, zai yi kyau a hakura mukamin ya tsaya a yankin Arewa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ban da Kudu maso kudu da Arewa ta yamma

Bayan zaben Godswill Akpabio da Barau Jibrin, kallo ya koma ga wanda zai zama shugaban masu rinjaye, kusan yankuna hudu su ke gaba a takarar.

Ana tsammanin daga Arewa maso gabas, Arewa maso tsakiya, Kudu maso gabas ko Kudu maso yamma za a samu sabon jagora a majalisar dattawan.

A duka mukaman da ke majalisar tarayya, ‘Yan Arewa maso tsakiya ba su tashi da komai ba. Legit.ng ta na tunanin za a ba su fifiko a wannan karo.

Ndume, Buhari, Bamidele

Rahoton ya ce wadanda su ke kang aba wajen neman wannan mukami sun hada da Sanata Ali Ndume, Opeyemi Bamidele da kuma Abdulfatai Buhari.

Kara karanta wannan

Hankalin Shugabannin Ma’aikatu ya Tashi a Sakamakon Zazzagar da Tinubu Yake yi

Ndume ya fito daga Arewa maso gabas, sauran biyu kuma Sanatocin Kudu maso yamma.

Sanata Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu ne Darektan yakin neman zaben Akpabio/Jibrin, mataimakinsa shi ne Sanatan na jihar Ekiti ta tsakiya.

An fara kuka a kan Akpabio yayin da ya yi nadin mukamai a ofishinsa, ana zargin sabon shugaban majalisar dattawan ya fifita Kiristoci da yankin Kudu.

Bola Tinubu zai yi zazzaga?

Ku na da labari cewa wasu shugabannin hukumomi su na rike da mukaman gwamnati tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya dare kan mulki.

Ana tunanin Bola Tinubu zai tsige wasu ko ya iya canza masu hukumomi, tuni har wasu sun fara murabus. Canjin gwamnati ya jawo dar-dar a ma'aikatu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng