Gwamnatin Tinubu Za Ta Samar Da Ayyuka Miliyan 1 Ga Matasan Najeriya, Kashim Shettima Ya Yi Bayani
- Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za ta samar da ayyukan yi miliyan 1 ga matasa
- Ya bayyana hakan ne a yayin taro da wata tawagar wakilci ta Shugaban kasar Koriya ta Kudu
- Kashim ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu za ta hada gwiwa da kasar Koriya ta Kudu wajen horar da matasa fasahohin zamani
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bayyana shirin gwamnatin tarayya na samar da ayyukan yi miliyan daya a bangaren fasahohin zamani.
Mataimakin shugaban kasar ya yi wannan jawabi ne a ranar Litinin, lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga Koriya ta Kudu, karkashin jagorancin dan aiken shugaban kasar, H.E. Jang Sungmin, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ya kuma jaddada aniyar Najeriya na ganin ta karfafa alaka da kasar Koriya ta Kudu, musamman wajen inganta harkokin kasuwanci, musayar fasahohi da kuma wanzar da zaman lafiya a duniya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Shettima ya ce za a fuskanci karancin ma'aikata a duniya
Shettima ya bayanna cewa nan da wasu 'yan shekaru masu zuwa, za a samu bukatuwa ta ma'aikata da za su cike wasu bangarori na fasaha a kasashen da suka ci gaba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar Shettima:
"A shirye muke mu yi hadin gwiwa da ku a fannin fasaha domin nan da shekarar 2030, za a samu gibin basira da kashi 65% a duniya, inda kasashen Amurka, Rasha da Brazil za su yi fama da gibin basira akalla miliyan shida. Na yi imanin Nijeriya tana da mutanen da ake bukata don cike wannan gibin basirar saboda kasarmu kasa ce ta matasa."
“Kashi 75 cikin 100 na ’yan Najeriya ba su wuce shekara 35 ba, don haka muna neman hadin kan ku da goyon baya wajen horar da matasanmu kan fasahohin zamani. Muna son samar da ayyukan yi miliyan 1 a bangaren fasahohin zamani."
Shettima ya kara da cewa kasar Indiya ta sami dala biliyan 120 a bara daga irin ayyukan da 'yan kasarta ke yi a sassa daban-daban na duniya, inda ya ce Najeriya ma za ta iya amfani da irin damar, kamar yadda Vanguard ta wallafa.
Shettima a cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran ofishinsa Olusola Abiola ya fitar, ya tabbatarwa gwamnatin kasar Koriya ta kudu kudurin gwamnatin Tinubu na yin hadin gwiwa da kasar don karfafa alaka tsakanin kasashen biyu.
Tinubu zai ziyarci Koriya ta Kudu a shekarar 2024
Ya kuma tabbatarwa da tawagar Koriyar cewa, Shugaba Tinubu zai amsa goron gayyatar takwaransa na Koriya, zuwa taron Afrika da Koriya a shekarar 2024.
Ya kara da cewa:
"Ina kuma tabbatar muku da cewa Najeriya na matukar godiya da goyon bayan da kasar Koriya ta Kudu ke ba ta a wurare da dama, irinsu babban taron majalisar dinkin duniya, a kokarinmu na samun kujera a kwamitin sulhu da sauran hukumomi na majalisar."
Shugaba Tinubu ya sauyawa filayen jiragen sama 15 suna zuwa sunayen wasu fitattun mutane
A wani labari da Legit.ng ta wallafa a baya, kun karanta cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya sauyawa wasu filayen jiragen sama suna zuwa sunayen wasu fitattun 'yan Najeriya.
Hakan na cikin yunkurin da shugaban yake yi na ganin ya yi wa harkar sufurin jiragen sama garambawul.
Asali: Legit.ng