Gwamna Alia Ya Biya Ma'aikatan Jihar Benue Albashi Bayan Shafe Watanni 7 Ba A Basu Ba A Baya

Gwamna Alia Ya Biya Ma'aikatan Jihar Benue Albashi Bayan Shafe Watanni 7 Ba A Basu Ba A Baya

  • Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya farantawa ma’aikatan jihar, bisa albashin da ya yi musu bayan shafe watanni bakwai
  • Gwamnan ya sha alwashin ci gaba da biyan ma’aikatan hakkokinsu da gwamnatin baya da ta shude ta hana su
  • Gwamnan ya ce hakan ya zamo wajibi, tunda ma’aikatan sun riga da sun yi aikin a baya

Benue - Gwamnatin jihar Benue ta sanar da biyan ma’aikatan jihar albashinsu karo na farko cikin watanni bakwai.

Da yake zantawa da jaridar The Cable, babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Benue, Tersoo Kula, ya ce an biya ma’aikata albashinsu na watan Mayu a ranar Lahadi.

Sannan Kula ya kuma ce za a biya ma’aikatan albashin watan Yuni nan ba da jimawa ba.

Gwamnan Benue ya biya albashin ma'aikata a karon farko
Gwamnan Benue Hyacinth Alia ya biya ma'aikatan jihar albashi bayan shafe wata 7 ba a ba su ba. Hoto: Fr. Alia TV Network
Asali: Facebook

Alia ya ce gwamnatin baya ta rikewa ma’akata albashi na tsawon lokaci

Kara karanta wannan

Zargin Batanci: Gwamnatin Sokoto Ta Bayyana Irin Matakin Da Za Ta Dauka Kan Masu Batanci Ga Annabi (SAW)

Ya kara da cewa gwamnatin da ta shude ta hana ma’aikata albashinsu na tsawon lokaci, amma gwamnati mai ci a yanzu, za ta yi kokarin biyansu dukannin hakkinsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani bangare na kalamansa na cewa:

"Da zarar mun biya albashin watan Yuni, za mu duba takardun domin mu ga abinda za mu yi game da sauran watannin da suke bin bashi."

Gwamnan ya yi alkawarin biyan ma’aikatan duka hakkokinsu

Da yake magana a yayin wani taro na manema labarai a jihar don tunawa da ranar dimokuradiyya, Hyacinth Alia, gwamnan jihar ta Benue, ya yi alkawarin fara biyan albashin ma’aikatan jihar daga ranar 25 ga watan Yuni.

A cewarsa:

“Mutanen Benue, muna sane da wahalhalun da al’ummarmu ke ciki musamman ma’aikatan gwamnati da wadanda suka yi ritaya saboda rashin biyansu albashi, fansho da kuma alawus-alawus.”

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan da Ake Zargi Ya Sace N70bn Ya Rabawa Mutane Goron Sallar N200m

“Muna kira da ku yi hakuri ku fahimce mu a yayin da muke aiki tukuru don magance wadannan matsalolin. Hakika, daga ranar 25 ga wannan wata, ma’aikatan gwamnati su fara sa ran jin shigowar kudadensu.”

Gwamnan ya kuma tabbatarwa al’ummar jihar cewa gwamnatinsa ba za ta ba ta lokacin wajen yi wa gwamnatin baya bita da kulli ba, kamar yadda jaridar The Sun ta ruwaito.

Buhari ya bayyana abinda ya hana ya cire tallafi kafin ya sauka mulki

Legit.ng ta kawo muku wani rahoto a baya kan dalilin da ya sanya tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari kin cire tallafin man fetur gabanin ya sauka mulki.

Buharin ya bayyana cewa saboda yana so dan takararsa na APC, Bola Ahmed Tinubu ya ci zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng