Gwamna Yusuf Ya Hana Ma'aikata Sama da 10,000 Albashi a Jihar Kano

Gwamna Yusuf Ya Hana Ma'aikata Sama da 10,000 Albashi a Jihar Kano

  • Gwamnan Kano ya dakatar da albashin ma'aikata sama da 10,000 waɗanda tsohon gwamna Ganduje ya ɗauka aiki
  • Akanta janar na jihar, Abdulsalam ya bayyana cewa ofishinsa zai gudanar da bincike don gano ma'aikata da aka ɗauka ba kan ka'ida ba
  • Ya tabbatar da cewa gwamnatin Abba ta biya kuɗin jarabawar NECO na ɗalibai sama da 60,000 a faɗin jihar Kano

Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya umarci Akanta Janar ya dakatar da albashin ma'aikata 10,800 waɗanda tsohon gwamna, Abdullahi Ganduje ya ɗauka aiki.

Gabanin ya karɓi madafun iko, gwamnatin Abba Gida-Gida ta zargi gwamnatin Ganduje da ɗaukar sabbin ma'aikata sama da 10,000 ba kan ƙa'ida ba yayin da wa'adin mulki ya zo dab da ƙarewa.

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.
Gwamna Yusuf Ya Hana Ma'aikata Sama da 10,000 Albashi a Jihar Kano Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Da yake hira da 'yan jarida a a Kano ranar Litinin, Akanta Janar, Abdulkadir Abdusalam, ya tabbatar da cewa mai girma gwamna ya umarci a cire ma'aikatan daga tsarin biyan albashi.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: An Gano Gwarwakin Ɗaliban Jami'ar Ahmadu Bello Zariya Bayan Awanni 48

Wane mataki gwamnan zai ɗauka kan ma'aikatan?

Abdulsalam ya ce ofishinsa zai gudanar da bincike mai zurfi domin gano sahihancin matakain da aka bi wajen ɗaukar ma'aikatan, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce binciken zai tabbatar da halastattu ma'aikata da kuma cire waɗanda tsohuwar gwamnati ta ɗauka ta haramtacciyar hanya.

Akanta Janar ɗin ya ƙara da cewa dukkan ma'aikatan kananan hukumomi da gwamnatin Ganduje ta ƙara wa girma zuwa matakin jiha, zasu ci gaba da samun albashin amma na matakin ƙananan hukumomi.

Haka nan ya umarci ma'aikatan da lamarin ya shafa su ci gaba da aiki a ma'aikatun da su ke a yanzu har zuwa lokacin da za'a kammala bincike.

Babu ma'aikaci ko ɗan fansho da za'a kara rage wa albashi - Abdulsalam

Mista Abdulsalami ya yi alkawarin cewa daga yanzu, babu wani ma'aikaci ko mai karɓan fansho da za'a cire wa wasu kudi ba gaira ba dalili kamar yadda ake yi a baya.

Kara karanta wannan

Eid El-Kabir: Shugaba Tinubu Ya Ayyana Ranaku 2 Don Hutun Babban Sallah

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin Abba Gida-Gida ta biya wa ɗaliban sakandire sama da 60,000 kuɗin zana jarabatar kammala sakandire (NECO), kamar yadda The Angle ta tattaro.

Gwamna Obaseki Ya Ba Dalibar da Ta Kafa Tarihi a Jami'ar LASU Aiki

A wani labarin na daban kuma Gwamna Obaseki na jihar Edo ya ɗauki ɗalibar da ta kafa tarihin shekara 40 a LASU aiki ba tare da bin wasu matakai ba.

Obaseki ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ɗauki Aminat Yusuf aiki ne domin toshe kowace ƙofa ga wasu jihohi da ka iya ɗauke ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262