Akwai Matsala: Jigo a Jam'iyyar PDP Ya Shirya Kwance Wa Jam'iyyar Zani a Kasuwa a Gaban Kotu

Akwai Matsala: Jigo a Jam'iyyar PDP Ya Shirya Kwance Wa Jam'iyyar Zani a Kasuwa a Gaban Kotu

  • Wani babban jigo a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ebonyi, ya shirya bada shaida akan jam'iyyar a gaban kotu
  • Prince Maurice Mbam ya bayyana cewa a shirye yake ya bayyana a gaban kotu ya bayar da shaida cewa jam'iyyar ta faɗi zaɓen gwamnan jihar
  • Ya musanta cewa zai koma jam'iyyar APC sannan ya yi kira da ƴan adawa jihar su daina yaɗa ƙarairayin da su ke akan gwamna Nwifuru

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ebonyi - Jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ebonyi kuma shugaban kwamitin amintattu na matasan Izzi Nnodo, Prince Maurice Mbam, ya yi iƙararin cewa jam'iyyarsa ba ta lashe zaɓen gwamnan jihar ba.

Jigon na jam'iyyar PDP a ranar Litinin, ya bayyana cewa a shirye yake ya bayyana a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar domin ya kawo hujjojinsa, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Wike Ya Kara Shiga Matsala Yayin Da Jam'iyyu 4 Suka Ayyana Yaki a Kansa

Jigon PDP zai watsa mata kasa a ido a kotu
Maurice Mbam ya ce zai bada shaida PDP ba ta ci zaɓe a Ebonyi ba Hoto: Prince Maurice Mbam
Asali: Facebook

Maurice Mbam ya kuma bayyana cewa gwamna Francis Nwafiru na jihar shi ne halastaccen wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.

Ya yi kira ga jam'iyyun adawa da su sakarwa gwamna Nwifuru mara

Da yake tattaunawa da manema labarai a birnin Abakaliki, Mbam ya yi kira ga jam'iyyun adawa na jihar da su daina yaɗa ƙarairayin da su ke yi akan gwamnan, su bar shi ya yi aikinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

"Gwamna ya yi sabbin naɗe-naɗe kuma har abubuwa sun fara kyau a jiha. Yakamata ƴan adawa su bar gwamnan ya yi aikinsa.
"A matsayinsa na wanda ya yi kakakin majalisa har na shekara takwas, ya san abubuwan da ke tafiya a jihar nan da inda kuma yake cike da matsaloli."

Ya musanta cewa zai koma APC

Mbam ya bayyana babu ƙamshin gaskiya cewa yana shirin tattara ƴan komatsansa ya koma jam'iyyar APC

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Babban Jigon Jam'iyyar APC Ya Rasu Kasa Da Wata Daya Bayan Barin Mulki

"Gwamna yana sauraron koken mutane. Ba gaskiya bane zan koma jam'iyyar APC nan bada daɗewa ba." A cewarsa.
"A shirye mu ke mu bayar da shaida cewa jam'iyyar PDP ta sha kashi a zaɓen. Muna sane da cewa maganar tana gaban kotu."

Jam'iyyu Hudu Sun Ayyana Yaki Akan Wike

A wani labarin na daban kuma, jam'iyyu huɗu sun haɗe kawunansu waje guda sun shirya yin fito na fito da tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike.

Jam'iyyun huɗu da suka haɗa da PDP, LP, NNPP da YPP sun fusata ne kan katsalandan ɗin da Wike yake son kawo wa a zaɓen shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng