Dan Majalisa Mai Hawa 7 Ya Zama Sabon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Yobe
- Hon Buba Chiroma Machiyo ya samu nasarar zama sabon kakakin majalisar dokokin jihar Yobe da ke Arewa maso Gabashin Najeriya
- Mashiyo ya samu nasara ne a zaɓen da aka gudanar a ranar Litinin, 26 ga watan Yuni a harabar zauren majalosae dokokin jihar
- Mashiyo shi ne dai ɗan takarar da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar ta ke goya wa baya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Yobe - Majalisar dokokin jihar Yobe ta yi sabon kakaki. Mambobin majalisar 24 a ranae Litinin, 28 ga watan Yuni, sun zaɓi Hon Buba Chiroma Machiyo a matsayin kakakin majalisar dokokin ta takwas.
Hon Machiyo, ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Jajere, shi ne zaɓin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sannan ɗan majalisar da ya fi kowa daɗewa a majalisar, inda ya fara zuwanta tun shekarar 1999.
Mashiyo dai bai taɓa shan kasho ba a takarar kujerar ɗan majalisar da ya yi ta mazaɓar Jajere. Ɗan majalisar sau bakwai yana lashe zaɓen da ya fito na kujerar ɗan majalisan dokokin jiha, cewar rahoton Aminiya.
Yadda Machiyo ya zama kakakin majalisar dokokin jihar Yobe
Magatakardan majalisar, Barr. Mohammed Alkali Yusuf, ya bayyana cewa majalisar ta samu takarda daga wajen gwamnan jihar, Mai Mala Buni, kan cewa ta yi zamanta na farko a ranar Litinin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Daga nan sai ya shirya zaɓe, inda dukkanin mambobin majalisar 24 suka kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen wanda ya samar da nasarar Machiyo.
Hon Adamu Dala Dogo, ɗan majalisa mai wakiltar Karasuwa, shi ne ya bayar da sunansa a matsayin ɗan takara, yayin da Hon Bukar Mustapha Timba, ɗan majalisa mai wakiltar Geidam ya mara masa baya.
Ƴan majalisar dokokin ta jihar Yobe sun kuma zaɓi, Hon Yau Usman Dachia, ɗan majalisa mai wakiltar Jakusko a matsayin mataimakin shugaban majalisar.
Matashi Ya Raba Kakakin Majalisar Jihar Yobe Da Kujerarsa
A baya rahoto ya zo kan yadda wani matashi mai shekara 35 ya kayar da kakakin majalisar jihar Yobe daga muƙaminsa a lokacin zaɓen 2023 da aka gudanar.
Lawan Musa na jam'iyyar PDP ya kayar da Ahmed Mirwa Lawan na jam'iyyar APC wanda shi ne kakakin majalisar a lokacin.
Asali: Legit.ng