Jigon PDP Ya Magantu Kan Batun Sauya Shekar Wike daga PDP Zuwa APC

Jigon PDP Ya Magantu Kan Batun Sauya Shekar Wike daga PDP Zuwa APC

  • Jigon APC a jihar Ribas, Augustine Wokocha, ya yi fatali da buƙatar tsohon gwamna Nyesom Wike na sauya sheka da jagorantar APC a jihar
  • Mista Wokocha ya nuna adawa da kiraye-kirayen Wike ya karɓi ragamar jam'iyyar APC reshen jihar Ribas idan ya baro PDP
  • Tun bayan hawan Bola Ahmed Tinubu kan gadon mulki, an ga Wike ya kai ziyara fadar shugaban kasa a lokuta da dama

Rivers - Fitaccen mamban APC kuma Kodinetan ƙungiyar kamfen Tinubu mai zaman kanta da aka rushe a jihar Ribas, Augustine Wokocha, ya ce baya adawa da Nyesom Wike ya dawo APC idan yana so.

Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas da ya gabata baya shiri da jam'iyyarsa PDP tun gabanin babban zaben 2023, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Wike tare da shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Jigon PDP Ya Magantu Kan Batun Sauya Shekar Wike daga PDP Zuwa APC Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Da yake zantawa da manema labarai a Patakwal, babban birnin jihar Ribas ranar Jumu'a 23 ga watan Yuni, Wokocha ya ce ba shi da matsala idan Wike ya zaɓi dawo wa cikin APC.

Kara karanta wannan

Manyan Jiga-Jigan PDP da Dubannin Mambobi Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC Ana Tunkarar Zaɓe a Jihar Arewa

Amma a cewarsa, zancen idan ya sauya sheka zuwa APC ya zama jagora ba ta taso ba domin jam'iyyar tana da jagora kuma ba ta buƙatar wani daban.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A rahoton Punch, Mista Wokocha, tsohon kwamishinan lantarki a jihar Ribas, ya ce:

"Dama haka siyasa take, don haka Wike ya sauya sheƙa zuwa APC ci gaba ne da zamu yi maraba da shi. Abun da ba zamu yarda da shi ba a ce Wike ne zai karɓi ragamar jam'iyya."
"Kar mu manta APC ce jam'iyyar da shi wanda ake ta habo-habon ya dawo cikinta ya maida mambobinta marasa galihu. Shi ne Wiken nan dai da ya ce APC na fama da cutar daji mataki na huɗu, PDP kuma ɗan zazzaɓi kawai ta kamu da shi."
"Amma duk da haka muna maraba da shi idan yana ganin cutar daji ya fi sauki fiye da zazzabin cizon sauron da yake fama da shi."

Kara karanta wannan

An Fara Maganar Shigowar Tsohon Gwamna Wike Daga PDP Zuwa Jam’iyyar APC

Tinubu: Babu Cire Tallafin Mai a Jawabin Ranar Rantsuwa Amma Na Sanar da Cire Wa

A wani labarin na daban kuma Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana yadda ya sanar da cire tallafin mai duk babu batun a cikin jawabin da aka shirya masa ranar rantsuwa.

Shugaban kasan ya ce sai bayan ya hau mumbarin magana ya ji cewa ya kamata ya cire tallafin tun a ranarsa da farko a Ofis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel