Gwamna Yahaya Bello Ya Karbi Dubannin Masu Sauya Sheka Zuwa APC a Jihar Kogi

Gwamna Yahaya Bello Ya Karbi Dubannin Masu Sauya Sheka Zuwa APC a Jihar Kogi

  • Dubannin mambobi da manyan kusoshin PDP a ƙaramar hukumar Ankpa ta jihar Kogi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
  • Gwamna Yahaya Bello ya tarbi dandazon masu sauya shekar a hukumance a gidan gwamnati da ke Lokoja
  • Ya tabbatar musu da cewa ba za a nuna musu banbanci ba, sun zama ɗaya da kowane mamban APC

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kogi - Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, a ranar Jumu'a, ya tabbatarwa al'umma cewa za'a gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓen gwamna ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.

Gwamnan ya yi wannan furuci ne yayin ƙarban dubannin mambobin PDP daga ƙaramar hukumar Ankpa, waɗanda suka sauya sheka zuwa APC, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Gwamna Yahaya Bello tare da masu sauya sheƙa.
Gwamna Yahaya Bello Ya Karbi Dubannin Masu Sauya Sheka Zuwa APC a Jihar Kogi Hoto: Kogi-Eyez/facebook
Asali: Facebook

Tsoffin jiga-jigai da mambobin babbar jam'iyyar adawa PDP sun aminta da komawa APC mai mulki kuma sun rusa duk wani tsarinsu zuwa cikin APC a Kogi.

Kara karanta wannan

Zulum Ya Sha Alwashin Daukan Mataki Kan Kisar Gillar Mutum 8 Da ISWAP Ta Yi A Borno

Kun zama ɗaya da kowane mamban APC

Bello ya tabbatar wa sabbin mambobin cewa su ɗauki kansu da matsayin 'yan gida domin ba za'a nuna banbanci tsakaninsu da sauran mambobin da suka taras a cikin APC ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ƙara da bayanin cewa APC reshen jihar Kogi jam'iyya ce da bata nuna fifiko ko banbanci a tsakanin 'ya'yanta, jaridar Guardian ta tattaro

Da yake yaba wa wakilan masu sauya shekar bisa sadaukarwa da jajircewa, Bello ya ce APC mai mulki ce jam'iyya ɗaya tilo da ya dace kowa ya dogara da ita.

Haka zalika gwamna Bello ya yaba wa tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar, Rabiu Alfa, bisa biyayyarsa da sadaukarwa, ya kuma gode wa Ciyaman din Ankpa, Ibrahim Abagwu.

Za'a gudanar da sahihin zaɓe a Kogi - Yahaya Bello

Gwamna Bello ya kara jaddada cewa APC bata nuna wariyar addini, kabila, matsayi ko wani abu da yake nuna banbanci tsakanin al'umma.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: Mutane da Yawa Sun Maƙale Yayin da Ambaliyar Ruwa Ta Shanye Rukunin Gidaje a Abuja

Ya ce:

"Ina ƙara baku tabbacin cewa za'a gudanar da sahihin zaɓe ranar 11 ga watan Nuwamba kuma cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali."
"Gwamnati zata tabbatar cewa ba'a tada hargitsi ba, zamu yi duk mai yuwuwa wajen ganin kowane ɗan Kogi ya kaɗa kuri'arsa lami lafiya domin duk wanda ya kawo hayaniya zai gamu da jami'an tsaro."

Gwamna Alia: Dole Mu Kwato Dukiyar Gwamnati da Tsohon Gwamna da Hadimansa Suka Wawure

A wani rahoton kuma Gwaman jihar Benuwai ya lashi takobin dawo da duk wata kadara da yake ganin tsohuwar gwamnati ta yi sama da faɗi da ita.

Hyacinth Alia ya kaddamar da kwamitin dawo da dukiyar gwamnati a matakin jiha da kananan hukumomi a Makurdi, babban birnin jiha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262