Gwamnan Ebonyi Ya Umarci Tsoffin Kwamishinoni Su Bar Gidajen Gwamnati
- Gwamnan jihar Ebonyi ya umarci tsoffin kwamishinonin Dave Umahi su gaggauta fita daga gidajen gwamnati
- A wata sanarwa da SSG ta fitar, gwamna Francis Nwifuru, ya basu wa'adin mako biyu daga nan zuwa 6 ga watan Yuli
- Rahoto ya nuna har yanzu wasu hadiman tsohon gwamna Umahi ba su bar rukunin gidajen kwamishinoni da ke Abakaliki ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Ebonyi - Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi ya umarci kwamishinonin tsohuwar gwamnatin da ta sauka su gaggauta tattara komatsansu su bar gidajen gwamnati.
Gwamnan ya ce ya basu wa'adin mako biyu, duk tsohon kwamishinan da ya san har yanzun bai fice daga rukunin gidajen kwamishinoni da ke Abakali ba, ya hanzarta fita.
Daily Trust ta tattaro cewa har yanzu wasu daga cikin kwamishinonin tsohon gwamna Dave Umahi na nan zaune a rukunin gidajen gwamnati duk da wa'adin mulkinsu ya ƙare.
Wannan ya haddasa yanayin wahala da ƙunci ga sabbin kwamishinonin da gwamna Francis Nwifuru, ya naɗa a sabuwar gwamnati mai ci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wa'adin kwana nawa gwamnan ya bai wa tsoffin kwamishinonin?
Umarnin mai girma gwamna na ƙunshe a wata sanarwa da sakataren gwamnati, Farfesa Grace Umezuruike, ta fitar, kamar yadda PM News ta ruwaito.
A sanarwan, gwamna Nwifuru ya bai wa tsoffin kwamishinonin Umahi daga nan zuwa 6 ga watan Yuli, 2023, duk wanda ya san bai tashi ba gaggauta tashi tun wuri.
SSG ta ce:
"Dogaro da umarnin mai girma gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, muna kira ga dukkan mazauna rukunin gidajen kwamishinoni su tashi daga wurin domin a bai wa sabbin kwamishinonin da aka naɗa."
"Muna masu ba da haƙuri idan hakan ya ɓata wa wani rai. Don haka muna rokon duk waɗanda umarnin nan ya shafa su gaggauta tashi cikin wa'adin mako biyu, daga 23 ga watan Yuni zuwa 6 ga watan Yuli."
Kwana biyu gabanin ya sauka daga mulki, Umahi ya raba wa hadimansa naira miliyan N800m a matsayin ladan da zasu nemi wurin zama bayan barin Ofis.
Mutane da Yawa Sun Maƙale Yayin da Ambaliyar Ruwa Ta Shanye Rukunin Gidaje a Abuja
A wani rahoton na daban kuma Gidaje da dama da motoci a rukunin gidajen Trade More sun nutse a ruwa sakamakon ambaliyar ruwa ranar Jumu'a.
Rahoto ya nuna mazauna yankin da ba'a san adadinsu ba har yanzu sun maƙale amma jami'an bada agaji sun duƙufa domin lalubo su.
Asali: Legit.ng