Batun Nadin Ministoci: Fitacciyar Lauya Ta Shawarci Tinubu Ya Gujewa Jiga-Jigan Kura-kurai 5 Da Buhari Ya Yi
An bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya guji aikata wasu daga cikin kurakuran da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya aikata a lokacin mulkinsa na 2015 da na 2019.
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Barista Titilope Anifowoshe a zantawarta da legit.ng, ta yi kira ga shugaban ƙasar da ya tabbatar da cewa abinda ya janyo gazawar gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bai sake maimaita kansa a gwamnatinsa ba a yayin da yake shirin kaddamar da ministocinsa a watan Yuli.
Ana dai sa ran cewa Shugaba Tinubu zai gabatar da sunayen ministocinsa a cikin kwanaki 60 na farkon mulkinsa kamar yadda sabuwar doka ta tanada.
A yayin da ake sa ran Tinubu zai yi aiki bisa doron kundin tsarin mulkin ƙasa, Anifowose, masaniyar shari’a, ta shawarci shugaban ƙasa da kar ya yi ƙoƙarin naɗa kansa minista, ko ƙoƙarin haɗe wasu ma'aikatun kamar yadda ya faru a gwamnatin baya.
Ga jerin shawarwarin da Anifowose ta bai wa Tinubu a ƙasa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
1. Kada Shugaba Tinubu ya naɗa kansa minista
Ta ce shugaban ƙasa yana da ayyuka da yawa a ƙasa da ya kamata ya yi. In da ta bayyana cewa Najeriya cike take da mutane masu hazaka da kishi waɗanda za su iya cike guraben muƙaman gami da gudanar da ayyuka yadda ake buƙata.
2. Kada Tinubu ya sake naɗa wani daga cikin ministocin Buhari
Masaniyar dokar ta kuma bai wa Tinubu shawarar cewa kada ya naɗa wani tsohon minista cikin ministocin gwamnatinsa da zai naɗa.
Ta ƙara da cewa bai kamata a ba ko ɗaya daga cikinsu muƙami ba, musamman in aka yi la'akari da yadda wasu daga cikinsu suka gudanar da ayyukan ofisoshinsu ba tare da an ɗauki wani mataki a kansu ba.
3. Kar Tinubu ya haɗe wasu ma’aikatun wuri guda
Lauyar ta kuma ce a bayyana yake cewa yunƙurin da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi na haɗe wasu ma'aikatu bai samar da abinda ake buƙata ba.
A kalamanta:
"Ya kamata a ce ma'aikatar matasa ta bambanta da ma'aikatar wasanni, kasafin kudi, tsare-tsare na kasa, da ma'aikatar kudi wasu ƙarin ma'aikatu ne da haɗesu bai samar mana da kyakkyawan sakamako ba."
4. Ya kamata Tinubu ya soke ministocin yanki
Barista Anifowoshe ta kuma ce ya kamata Shugaba Tinubu ya yi ƙoƙarin soke duk wasu ministocin yanki da ake da su, inda ta ce hakan zai taimaka wajen haɗin kan 'yan ƙasa.
Lauyar ta kuma ƙara da cewa kundin tsarin mulkin ƙasa ya riga da ya yi bayani game da cewa 'dukanmu ɗaya muke'.
5. Waɗanda ya kamata Shugaba Tinubu ya naɗa ministoci
Shahararriyar masaniyar dokar ta kuma bayyana cewa bai kamata Shugaba Tinubu ya taƙaita naɗin ministocinsa ga ‘yan siyasa kaɗai ko kuma ga masana kawai ba.
Ta ce ya kamata rabon muƙaman nasa ya zagaya ko ina cikin ƙasa, kuma ya yi ƙoƙarin naɗa duka masanan da kuma 'yan siyasa.
Cikakken jerin ministocin da ake sa ran Tinubu zai naɗa nan ba da jimawa ba
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan cikakken jerin ministocin da ake sa ran Tinubu zai naɗa kafin ranar 28 ga watan Yulin 2023.
Sunayen mutane 27 ne dai ake ganin Tinubu zai miƙa majalisa domin a tantancesu kafin su zama ministoci.
Asali: Legit.ng