Karin Albashin Tinubu, Shettima Da Sauran 'Yan Siyasa, Shehu Sani Ya Yi Tsokaci
- Sanata Shehu Sani, tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa, ya yi martani dangane da ƙara albashin 'yan siyasa da aka yi
- Hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta Najeriya (RMAFC) ce ta sanar da ƙarin albashin manyan 'yan siyasa da kashi 114%
- Sanatan ya ce bai kamata a ƙara albashin manyan ba kafin a ƙara na ƙananun ma'aikata da galibinsu talakawa ne
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya yi martani dangane da ƙarin albashin da hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta ƙasa (RMAFC), ta yi wa 'yan siyasar Najeriya.
A yau ne dai hukumar tattara kudaden shiga ta ƙasa (RMAFC) ta amince da ƙarin albashin 'yan siyasar Najeriya da kaso 114%, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Mutanen da ƙarin kaso 114% zai shafa
Waɗanda ƙarin zai shafa sun haɗa da shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, gwamnoni da 'yan majalisun jihohi da na tarayya da kuma ma'aikatan ɓangaren shari'a.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Karin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsaka da batun cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi, da kuma batun ƙarin mafi karancin albashin ma'aikata daga naira dubu 30 zuwa sabon abinda aka yanke.
Shehu Sani ya yi martani kan ƙarin
Da ya ke martani game da batun a shafinsa na Tuwita, Shehu Sani ya ce bai kamata a fara ƙara albashin manyan ƙasa ba tare da an fara ƙara na ƙananun ma'aikata talakawa ba.
Shehu ya ƙara da cewa, ƙarin albashin da kaso 114 na nufin, ɗan Majalisar Wakilai zai riƙa karɓar sama da linkin kuɗaɗen da yake karɓa a da a wata.
A kalamansa:
“Ƙara albashin ƙananun ma'aikata ya kamata a fara yi, ba na manya da ke manyan ofisoshi ba.”
“Da wannan ƙarin na 114%, ɗan majalisar tarayya zai riƙa karɓar naira 2m a matsayin albashinsa, da kuma naira 25m a matsayin kuɗaɗen tafiyar da ofis.”
“Ya kamata a kashe kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafi yadda ya kamata.”
Tinubu, Shettima da manyan 'yan siyasa sun samu ƙarin kaso 114 a albashinsu
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan cewa hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta ƙasa (RMAFC), ta amince da ƙara albashin manyan yan siyasa da kashi 114%.
Hakan dai na zuwa ne a lokacin da ake ta ƙoƙarin ganin an ƙarawa ƙananun ma'aikatan Najeriya albashi zuwa daidai da yadda zai daidaita da yanayin buƙatunsu.
Asali: Legit.ng