“Ka Kyale Wike Ya Koma APC”, DG Na Kungiyar APC Ga Fubara

“Ka Kyale Wike Ya Koma APC”, DG Na Kungiyar APC Ga Fubara

  • An bukaci gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara da ya kyale magabacinsa, Nyesom Wike ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki
  • Kungiyar ASAF na APC ce ta yi wannan kiran a ranar Laraba, 21 ga watan Yuni, sannan ta bukaci Fubara da ya mayar da hankali kan nasarar gwamnatinsa
  • Kungiyar na martani ne ga rokon Wike da Fabura ya yi, inda ya bukace shi da kada ya guje masa koda ya koma daya bangaren a siyasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Kungiyar yan majalisar jiha na APC ta bukaci gwamnan jihar Ribas, Sim Fubara da ya kyale tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike ya tafi zuwa inda yake muradi a bangaren siyasarsa.

Hakan ya biyo bayan rade-radin da ake yi cewa watakila Wike ya gama tsare-tsare domin sauya sheka daga jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Jigon PDP Bode George Zai Koma Wajen Tinubu a APC? Gaskiya Ta Bayyana

Jiga-jigan jihar Ribas
“Ka Kyale Wike Ya Koma APC”, DG Na Kungiyar APC Ga Fubara Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

A cewar kungiyar, ya kamata Gwamna Fubara ya kyale Wike ya yanke shawara game da mataki na gaba da yake son dauka a siyasarsa sannan ya mayar da hankali kan gudanar da mulkin jihar mai arzikin man fetur.

APC a shirye take ta tarbi Wike, inji kungiyar

A wata sanarwa da ya saki a ranar Talata, 20 ga watan Yuni, a Abuja, Darakta Janar na kungiyar ASAF, Ambasada Fubara Dagogo, ya bayyana cewa a shirye APC take ta tarbi Wike a cikinta sannan ta kwankwadi tarin saninsa a siyasa da shugabanci, rahoton Vanguard.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wike dai ya juyawa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyarsa, Atiku Abubakar baya a lokacin zaben 2023 sannan ya marawa Asiwaju Bola Tinubu na APC baya kuma shine ya lashe zaben.

Bayan rantsar da Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya, an sha ganin Wike a fadar shugaban kasa tare da wasu mambobin APC lamarin da ya kara rura wutar rade-radin cewa yana shirin sauya sheka.

Kara karanta wannan

An Ba Abba Gida-Gida Wa’adin Awanni 72 Ya Dakatar Da Rushe-Rushe a Kano, Cikakken Bayani

Kan haka ne, gwamnan na jihar Ribas mai ci ya bukaci magabacin nasa da kada ya guje masa koda ya ketara zuwa daya bangaren a siyasa, rahoton Channels TV.

Yan Najeriya za su yi kukan dadi cikin watanni 6 masu zuwa, malamin addini

A wani labari na daban, Prophet Jeremiah Omoto Fufeyin na cocin Christ Mercyland Deliverance Ministry ya yi hasashen cewa yan Najeriya su tsammaci tarin ci gaba a watanni shida masu zuwa na gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu.

Malamin ya yi tinkaho cewa duk faston da kalamansa basu faru ba bai kamata a dunga daukarsa a matsayin babban fasto ba, yana mai cewa ya yi hasashen nasarar jam'iyyar APC a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng