Kotu Ta Mayar Da Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara Kan Mukaminsa
- Wata babbar kotun tarayya a birnin tarayya Abuja ta zartar da hukunci kan ƙarar da tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara ya shigar
- Mahadi Aliyu Gusau a ƙarar ya ƙalubalanci tsige shi daga muƙaminsa da majalisar dokokin jihar Zamfara ta yi
- Kotun ta mayar da Mahadi kan muƙaminsa na mataimakin gwamnan jihar tun daga lokacin da ya shigar da ƙarar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya mai zamanta a birnin tarayya Abuja, ta mayar da Mahadi Aliyu Gusau a matsayin mataimakin gwamnan jihar Zamfara.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Gusau da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun shigar da ƙara ne kan hanyar da majalisar dokokin jihar ta bi ta tsige shi daga muƙaminsa a watan Fabrairun 2022.
Da yake zartar da hukuncinsa a ranar Laraba, mai sharia Inyang Ekwo ya bayyana cewa kwamitin bincike da tsohon gwamnan jihar Bello Matawalle ya kafa ya saɓa doka, cewar rahoton The Cable.
Kotun ta bayar da umarnin a mayar da shi kan muƙaminsa
Alƙalin ya bayar da umarnin mayar da Mahadi muƙamin mataimakin gwamna tun daga ranar da ya shigar da ƙara a watan Yulin 2021.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kuma kawar da dukkanin matakai da hanyoyin da aka bi wajen tsige mataimakin gwamnan a lokacin da ƙarar ta ke a gaban kotun.
"A dalilin hakan an bayar da umarnin mayar da wanda ya shigar da ƙara (Mahadi Aliyu Mohammed) kan muƙaminsa na mataimakin gwamnan jihar Zamfara, tun daga ranar 8 ga watan Yulin 2021 lokacin da aka fara sauraron wannan ƙarar." A cewar alƙalin.
"An kuma bayar da umarnin jingine duk wani hukunci da waɗanda ake ƙarar suka ɗauka wajen tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara, a lokacin da wannan ƙarar ta ke a gaban kotun nan.
A Bashi Na Ke Gudanar Da Mulkin Zamfara, Gwamna Dauda Lawal
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare ya bayyana halin da ya zo ya tsinci asusuwan ajiya na jihar Zamfara. Gwamnan ya ce ya zo ya tarar babu ko sisi a lalitar jihar.
Dauda Lawal ya ce tsohon gwamna Matawalle ya ƙarar da komai, inda a asusu ɗaya ne kawai aka samu N3m zuwa N4m a cikinsa.
Asali: Legit.ng