Jerin Sunayen Masu Mukamai 10 A Lokacin Buhari Da Ya Kamata Tinubu Ya Bincika, Bayanai Sun Fito
- Tsohon mataimakin sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC na ƙasa, Timi Frank, ya bayyana sunayen masu muƙamai a lokacin Buhari da bai kamata binciken EFCC ya tsallake ba
- Frank ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya tabbatar da cewa ‘yan majalisar ministocin Buhari da ake zargi da cin zarafin ofisoshinsu sun fuskanci hukunci
- Jigon na APC ya ambaci sunayen Abubakar Malami, Hadiza Bala, Hadi Sirika, da sauran masu muƙamai da yawa da ya kamata Shugaba Tinubu ya bincika
Abuja - Tsohon mataimakin sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC na ƙasa, Tuni Frank, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu, da ya binciki wasu masu manyan mukamai na tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Frank a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 20 ga watan Yuni, ya ce ya kamata Tinubu ya gudanar da bincike a kan zargin cin zarafin ofishin wasu daga cikinsu, kuma kada a bari su gujewa hukunci, in ji Daily Independent.
Jigon na APC ya bayyana sunayen ‘yan majalisar ministocin Buhari da ya kamata su kasance a komar Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC), da kuma Hukumar Jami'an Tsaro Na Farin Kaya (DSS).
Jerin sunayen masu muƙamai lokacin Buhari da ya kamata shugaba Tinubu ya bincika
A cewar Timi Frank, sunayen masu muƙamai a lokacin Buhari da ya kamata a bincika kamar yadda jaridar The Punch ta tattaro su ne:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
1. Timipre Sylva - Tsohon ƙaramin ministan albarkatun man fetur, kuma ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa, a watan Nuwamban 2023.
2. Sanata Hadi Sirika - Tsohon ministan sufurin jiragen sama.
3. Abubakar Malami - Tsohon babban lauyan Gwamnatin Tarayya kuma ministan shari'a.
4. Mele Kyari - babban jami'in kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL).
5. Sadiya Umar Farouq - Tsohuwar ministar harkokin jin ƙai da kula da ci gaban al’umma.
6. Hadiza Bala Usman - Tsohuwar shugabar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya (NPA), yanzu haka ita ce mai ba shugaban ƙasa shawara ta musamman kan harkokin siyasa.
7. Col. Hammid Ali - Tsohon kwanturola janar na hukumar kwastam ta Najeriya.
8. Bashir Jamo - Babban jami’in Hukumar Kula da Tsaron Ruwa ta Najeriya (NIMASA).
9. Tsofaffin manajan daraktoci da shuwagabannin Hukumar Raya Yankin Neja-Delta (NDDC).
10. Duka shugabannin tsaron da aka yi wa ritaya cikin kwanakin nan.
Frank ya shawarci Tinubu game da gwamnonin PDP da ke nuna masa goyon baya
Frank ya kuma shawarci Tinubu da ya yi hattara da tsaffin gwamnoni, musamman na jam’iyyar PDP, waɗanda a yanzu suke nuna suna goyon bayan gwamnatinsa.
Ya bayyana cewa buƙatun kansu ne suka kawo su, ya kuma gargaɗi Tinubu da kada ya bari gwamnatinsa ta zama matattarar sanannun barayin ƙasa.
Sannan ya ce, duk da cewa har yanzu ana kotun sauraron ƙararrakin zaɓen don tantance haƙiƙanin sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata, ‘yan Najeriya za su yabawa Tinubu a inda ya yi daidai, sannan kuma su yi ƙorafi idan ya yi kuskure.
Shugaba Tinubu ya isa Faransa wajen taron tattalin arzikin duniya
Legit.ng ta kawo muka labarin cewa, shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya tafi ƙasar Faransa domin halartar wani taron tattalin arziƙi na duniya.
Da yammacin ranar Talata, 20 ga watan Yuni ne aka tabbatar da labarin saukar jirgin shugaban a birnin Paris.
Asali: Legit.ng