'Za Ka Iya Cin Zabe A Gaba,' Dan Majalisar Jam'iyyar Labour Ya Shawarci Peter Obi Ya Marawa Tinubu Baya

'Za Ka Iya Cin Zabe A Gaba,' Dan Majalisar Jam'iyyar Labour Ya Shawarci Peter Obi Ya Marawa Tinubu Baya

  • Dan majalisar makilai, ƙarƙashin jam'iyyar Labour, Amobi Ogah, da ke wakiltar mazaɓun Isuikwuato da Umunneochi da ke jihar Abia ya bai wa Peter Obi shawara
  • Ɗan majalisar ya ce yanzu lokacin zaɓe ya riga da ya wuce, ya kamata duk masu adawa da zaɓin Shugaba Tinubu su zo su yi mubaya'a
  • Ya ce ya zama wajibi a mutunta duk wanda Allah ya ɗorawa nauyin shugabantar talakawan Najeriya, kuma a ba shi goyon baya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Wani mamba a Majalisar Wakilai ƙarƙashin jam'iyyar Labour, Amobi Ogah, ya bai wa ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar ta sa, Peter Obi shawara kan Tinubu.

Ɗan majalisar, da ke wakiltar mazaɓun Isuikwuato da Umunneochi da ke jihar Abia, ya yi kira ga Peter Obi da ya zo ya marawa Tinubu baya.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Yi Martani Mai Zafi Ga Wike Bisa Ikirarin Cewa An Sanya Masa Guba a Sakatariyar PDP

Ya bayyana hakan ne a yayin da yake hira da 'yan jarida a Abuja, kamar yadda Premium Times ta wallafa.

Dan Majalisar Wakilai na jam'iyyar Labour ya nemi Obi ya mutunta Tinubu
Dan Majalisar Wakilai ƙarƙashin jam'iyyar Labour, ya shawarci Peter Obi ya ba Tinubu goyon baya. Hoto: Peoples Gazette
Asali: UGC

Ya shawarci Peter Obi da kar ya sare, amma ya bai wa Tinubu goyon baya

Ya ce a hidimar siyasa ba a sarewa idan mutum bai yi nasara ba. Ya ce kar mutum ya ɗauka cewa don bai yi nasara a yanzu ba shikenan a gaba ma ba zai yi ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sannan ya ce da zarar an sanar da wanda ya lashe zaɓe, to lallai ne mutum ya yi mubaya'a muddun dai yana so ya zama ɗan siyasa na gari.

Duk da dai ɗan majalisar bai kama suna ba a jawabin nasa, mutane da dama na ganin da Peter Obi yake, wanda ya sha kaye hannun Tinubu na jam'iyyar APC, a zaɓen 25 ga watan Fabrairun 2023 da ya gabata.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sallami Hafsoshin Tsaro da IGP Daga Aiki, Ya Naɗa Sabbin Da Zasu Maye Gurbinsu

A yanzu haka dai Peter Obi da sauran wasu 'yan takara na ƙalubalantar sakamakon zaɓen Tinubu a kotun sauraron ƙararrakin zaɓe.

Dan majalisar ya nemi a mutunta Shugaba Tinubu

Mista Ogah ya ƙara da cewa dole ne a mutunta Shugaba Tinubu a yayin da ake jiran sakamakon da kotu za ta yanke kan zaɓen nasa, kamar yadda Peoples Gazette ta wallafa.

Ya ƙara da cewa lokacin zaɓe ya riga da ya wuce, yanzu lokaci ne na gudanar da mulki, kuma dole ne a mutunta duk wanda Allah ya bai wa shugancin.

A kalamansa:

“A saboda haka ne nake yawan cewa, duk wanda Allah ya ɗora akan kujerar nan, to ka bashi goyon baya har zuwa lokacin da kotu ko Ubangiji ya yi hukunci.”
“Dole ne mu sanya Najeriya a gaba. Najeriya ta fi kowa muhimmanci. Tana da muhimmanci fiye da ni kai na. Bari in faɗa muku, Allah ne kaɗai ke ba da mulki.”

Kara karanta wannan

Dan Sandan Da Ya Dawo Da $800 Na Wata Hajiya a Katsina, Ya Samu Kyautar Da Ba Zai Taba Mantawa Da Ita Ba a Rayuwarsa

Malamin addinin ya hasaso abinda zai faru nan da wata 6 a mulkin Tinubu

Legit.ng ta kawo muku rahoto a baya kan wani malamin addinin Kiristanci, Prophet Jeremiah Omoto Fufeyin da ya bayyana abubuwan da ya hasaso cewa za su faru a watanni shida masu zuwa a gwamnatin Tinubu.

Ya ce 'yan Najeriya su tsammaci ganin abubuwa na ci gaba a cikin wadannan watannin shida masu zuwa na mulkin Shugaba Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng