Naira Miliyan 4 Kacal Na Tarar a Asusun Gwamnatin Zamfara, Gwamna Dauda Lawal Dare Ya Yi Ƙarin Haske

Naira Miliyan 4 Kacal Na Tarar a Asusun Gwamnatin Zamfara, Gwamna Dauda Lawal Dare Ya Yi Ƙarin Haske

  • Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya koka kan yadda ya ce gwamnatin baya ta yashe asusun jihar gabanin barinta ofis
  • Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin da ta shuɗe miliyan 4 kacal ta bari a cikin asusun gwamnatin jihar
  • Ya ce tunda ya karɓi mulki da bashi yake tafiyar da duka ayyukan gwamnatinsa, inda ya kuma koka kan rashin biyan albashin ma'aikata

Gusau, jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya koka kan yadda yace gwamnatin da ta shuɗe ta baya bata bar kuɗaɗe a lalitar gwamnatin jihar ba.

Ya ce ya zo ya tarar da an kwashe kusan komi a cikin asusun jihar, inda bai wuce naira miliyan 3 zuwa 4 ba ne ya tarar a lokacin da ya amshi mulki.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Yi Martani Mai Zafi Ga Wike Bisa Ikirarin Cewa An Sanya Masa Guba a Sakatariyar PDP

Gwamna Dauda Lawal ya ce ba a bar masa komai ba a asusun jihar Zamfara
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya ce a kan bashi yake tafiyar da jihar. Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Kan basussuka nake tafiyar da gwamnatina, cewar Dauda Lawal

Dauda ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC, inda ya bayyana cewa akan basussuka yake tafiyar da jihar tun bayan hawansa mulki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dauda ya kuma ƙara da cewa a yanzu haka ma'aikatan gwamnati jihar, sun shafe watanni uku ba tare da albashi ba.

Ya ce in da zai samu naira biliyan 20 da gwamnatin baya ke iƙirarin ta bari a asusun jihar, to da lallai zai biya albasin ma'aikata da su.

Abubuwa da dama a jihar sun tsaya cak

Bugu da ƙari, gwamnan ya ce akwai abubuwa da dama da basa gudana a jihar saboda rashin kuɗi.

Daga ciki akwai ma'aikatun gwamnatin jihar da yanzu haka babu wutar lantarki saboda rashin biyan kudin wuta.

Kara karanta wannan

Sabon Gwamnan Arewa Ya Yi Shiga Mai Ban Mamaki, Ya Kai Ziyarar Bazata Wani Asibiti a Keke Napep

Gwamnan ya kuma koka kan cewa yanzu haka jami'an tsaro na bin jihar basussuka na alawus-alawus ɗin da ake ba su har na tsawon watanni uku.

Haka nan ya kuma ya ƙara da cewa, ɗaliban sakandiren jihar ta Zamfara ba su samu damar rubuta jarabawar WAEC da NECO ba duk a dalilin hakan.

Da yake magana kan matsalar ruwa da jihar ke fuskanta, ya ce jihar ta kwashe watanni aƙalla huɗu ba tare da isasshen ruwan sha ba.

Gwamnan ya ce sai da ya ciyo bashi sannan ya samu kuɗaɗen da ya yi amfani da su wajen fara magance matsalar ruwan sha a jihar, kamar yadda The Cable ta wallafa.

Wani ɓangare na kalamansa na cewa:

“Ba zan iya cewa na magance matsalar ruwan sha a Zamfara ba amma zan yi iyakar ƙoƙarina don ganin na magance matsalar.”

Gwamna Dauda Lawal ya sha alwashin biyan albashi kafin sallah

Kara karanta wannan

Rusau: NITP Ta Gargadi Gwamnatin Kano Kan Tsagaita Rushe-rushe, Ta Bayyana Irin Asarar Da Aka Tafka

Gwamna Dauda Lawal ya sha alwashin biyan ma'aikatan jihar ta Zamfara, albashinsu gabanin bikin babbar sallah da ke ƙaratowa.

Ya ce zai yi iya duk mai yiwuwa wajen ganin ya biya ma'aikatan bashi na albashinsu da suke bin gwamnatin jihar.

Bana cikin mutanen da EFCC ke nema, Matawalle ya yi bayani

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa a baya, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana cewa babu sunansa a cikin jerin mutanen da EFCC ke nema ruwa a jallo.

Mai taimakawa tsohon gwamnan kan harkokin yaɗa labarai Lawal Umar, ya bayyana cewa labarin da aka wallafa da ke nuna cewa ana nemansa ba ya da tushe balle makama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng