Alkalan Kotun Karar Zaben 2023 Sun Yi Fatali da Rokon Lauyoyin APC, Bola Tinubu

Alkalan Kotun Karar Zaben 2023 Sun Yi Fatali da Rokon Lauyoyin APC, Bola Tinubu

  • Jam’iyyar APM ba ta janye karar da ta shigar a gaban kotun da yake sauraron shari’ar zaben 2023 ba
  • Lauyoyin APM da ‘dan takararta a zaben shugaban kasa sun ce Kashim Shettima ya shiga takara biyu
  • APC da Bola Tinubu su na so a soke karar da aka gabatar, Alkalan kotun sun ki yarda da bukatar nan

Abuja - Kotun da ke sauraron karar zaben shugaban kasa da aka yi a 2023 a Najeriya, bai karbi daya daga cikin bukatar wadanda ake tuhuma ba.

A yammacin Litinin, rahoto ya zo daga Daily Trust cewa Alkalan kotun da ke sauraron korafin zaben ya ki yarda a rusa karar jam’iyyar APM.

Lauyoyin da su ke kare Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyarsa ta APC mai-ci su na so ayi waje da korafin da laiyoyin APC su ka shigar a gaban kotun.

Kara karanta wannan

Abin Da Ya Jawo Mu Ka Hallara Majalisa Tun Karfe 4:00 Na Asuba, In Ji Sanatan APC

Tinubu
Kamfen Bola Tinubu a Legas Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Alkalan da su ka saurari zaman yau a karkashin jagorancin Haruna Tsammani, sun nuna cewa watsi da karar APM zai nuna babu adalci a shari’ar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ba za a kora karar APC ba - Haruna Tsammani

Mai shari’a Haruna Tsammani ya nuna dole a ba kowane bangare damar ya gabatar da korafinsa. The Cable ta ce APC ta ki janye karar da ta shigar.

Jam’iyyar hamayya ta APM da ‘dan takararta, Chichi Ojei sun shigar da kara a kotun zaben su na dogara da cewa Kashim Shettima ya shiga takara biyu.

Jaridar ta ce Lauyoyin da su ka tsayawa APM su na ikirarin Sanata Shettima ya nemi takarar majalisar dattawa da na mataimakin shugaban kasa.

Hujjar Jam'iyyar APC

Babban lauyan shugaban kasa wanda ya yi wa APC takara a zaben 2023, Wole Olanipekun (SAN) ya kafa hujja a kotu da hukuncin da kotun koli ta yi.

Kara karanta wannan

Yan Gidan Magajiya Sun Harzuka Sun Maka Kwastoma A Kotu Kan Tura Musu Alat Na Bogi Bayan Sun Gama Harka

A watan Mayu ne Alkalan kotun koli su ka yi watsi da karar da PDP da shigar a kan Shettima, ta ce jam’iyyar ba ta da hurumin kalubalantar lamarin.

ICRI ta rahoto cewa Haruna Simon Tsammani da sauran abokan aikinsa ba su karbi wannan hujja ba, su ka ce kotu za ta saurari abin da ke tafe da APM.

Gideon Ijiagbonya wanda shi ne Lauyan jam’iyyar adawar ya shaidawa Alkalan cewa ya samu hukuncin kotun koli, amma ya hangen nasara a kararsa.

Abubakar Malami ya tsere?

Labari ya zagaye gari cewa tsohon AGF ya na wasan buya da EFCC bayan hawan Bola Tinubu. An ji labari Abubakar Malami ya musanya wannan batu.

Abubakar Malami SAN ya ce EFCC ko wata hukuma ba ta kira shi ba, kuma idan an nemi shi zai mika wuya, Lauyan ya ce bai da dalilin barin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng