Jam'iyyar APC Ta Bayyana Abinda Zai Faru Da Aregbesola Da Wadanda Suka Ci Amanar Tinubu, Oyetola a Jihar Osun

Jam'iyyar APC Ta Bayyana Abinda Zai Faru Da Aregbesola Da Wadanda Suka Ci Amanar Tinubu, Oyetola a Jihar Osun

  • Shugabannin jam'iyyar APC a jihar Osun sun bayyana abinda da zai faru da ƴaƴan jam'iyyar waɗanda suka ci amanar tsohon gwamna Oyetola da Tinubu
  • Tajudeen Lawal, shugaban jam'iyyar APC na jihar ya yi fatali da batun cewa manyan ƴan jam'iyyar sun nemi tsohon gwamna Aregbesola ya nemi yafiya ya dawo jam'iyyar
  • Lawal ya ce jam'iyyar bata yanke hukunci kan yadda za ta hukunta Aregbesola ba amma ya yi nuni da cewa ba ɗaga ƙafa ga waɗanda suka ci amanar jam'iyyar

Jihar Osun - Tsohon gwamnan jihar Osun kuma tsohon ministan shugaba Buhari, Rauf Aregbesola, baya ga tsuntsu baya ga tarko kan hukuncin da zai faɗa masa dangane da zamansa ɗan jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Shugaban jam'iyyar APC a jihar, Tajudeen Lawal, ya bayyana cewa ƴaƴan jam'iyyar da suka ci dunduniyarta a lokacin zaɓen gwamna da na shugaban ƙasa a jihar, za su fuskanci hukunci, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Faɗi Babban Jigon da Alamu Suka Nuna Zai Koma APC, Ya Roƙe Shi Alfarma 1

Jam'iyyar APC a Osun za ta hukunta wadanda suka ci amanarta
Jam'iyyar APC a Osun ta sha alwashin hukunta waɗanda suka ci dunduniyarta Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Gboyega Oyetola, RAUF AREGBESOLA
Asali: Facebook

"Waɗanda suka ci dunduniyar jam'iyya za su ji a jikinsu" A cewar shugaban

Lawal ya bayyana hakan ne a wajen wani taro na musamman da aka shirya domin tarbar ƴan mazaɓar Ilesa waɗanda suka yi aiki a majalisun jiha da na tarayya da gwamnatin tsohon gwamna Gboyega Oyetola, a ranar Lahadi, 18 ga watan Yuni a birnin Ilesa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Babu ɗan jam'iyya wanda ya ci dunduniyar mu a lokacin zaɓen gwamnan da ya gabata da babban zaɓen jihar nan da za mu ɗaga wa ƙafa." A cewarsa.

Jam'iyyar APC a Osun ta yi fatali da batun shawarar dattijanta kan Aregbesola

Lawal ya musanta batun cewa dattijan jam'iyyar sun nemi tsohon ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, ya nemi yafiya ta haƙiƙa domin ya sake dawowa cikin jam'iyyar, rahoton PM News ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugabannin Jam'iyyar PDP Sun Yi Murabus Tare Da Ficewa Daga Jam'iyyar, Sun Bayyana Dalilansu

Ya kuma yi fatali da shawarar da Aregbesola ya kawo ta a sake fasalin jam'iyyar a jihar.

Gwamna Fubara Ya Nemi Alfarmar Wike

A wani labarin gwamnan jihar Rivers Siminalayo Fubara, ya roƙi tsohon gwamnan jihar alfarmar kada ya yi nesa da shi ko da ya fice daga jam'iyyar APC.

Fubara ya nemi alfarmar nan yayin da alamu su ke ta ƙara nuni da cewa Nyesom Wike zai iya ficewa daga jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel