Yadda Peter Obi Ya Ci Amanar Atiku Abubakar Gabanin Zaben Shugaban Kasa Na 2023, Sabbin Bayanai Sun Fito
- An zargi Peter Obi, ɗan takarar shugabanci ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar Labour, da aikata cin amana da kuma yaudara
- Fasto Adewale Giwa na cocin 'The Second Coming of Christ' ne ya bayyana haka a yayin da yake gabatar da huɗuba a ranar Lahadi, 18 ga watan Yuni
- Ya bayyana cewa ƙorafe-ƙorafen Peter Obi akan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a kotun sauraron ƙararrakin zaɓe a matsayin ɓata lokaci
An zargi ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023 da ya gabata, Peter Obi, da cin amanar tsohon ubangidansa, Alhaji Atiku Abubakar, ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar PDP.
Kamar yadda Sahara Reporters ta tattaro, Fasto Adewale Giwa na cocin 'The Second Coming of Christ Ministry' ne ya yi wannan zargi a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni.
Giwa ya ce ƙarar da Peter Obi ya shigar ba ta da amfani
Giwa ya bayyana cewa ƙarar da Peter Obi ke ci gaba da yi a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ba wai so yake a soke nasarar da shugaba Bola Tinubu ya samu a rumfunan zaɓe ba, ya je ne kawai don jin daɗi da kuma zugasa da ake yi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yace:
“Lokacin da ba lokacinka bane, to fa ba naka ba ne! Ya ci amanar ubangidansa, Atiku, wanda ya fito da shi aka sanshi.”
"Idan da gaske kana son Najeriya sosai kamar yadda ka shelanta, me ya sa ba ka tsaya cikin jam'iyyarka don ai yaƙi tare da kai ba? Sai dai kawai aka ji ka canza jam'iyya, kamar ba ka cikin tsarin da ya kai mu inda muke a yau.”
Ya bayyana Obi a matsayin mayaudari kuma mutum mai girman kai a lokacin da yake kawo hujja daga littafin Proverbs 16:5.
Giwa ya ce:
“Ubangiji ba ya barin mai girman kai, munafunci, da cin amana ba, in ji Proverbs, sura ta 16 aya ta 5. Ubangiji ya ce zai sanyasu a inda ya dace.”
"Mun san duk 'yan siyasar da za mu ɗorawa alhaki idan wani abu ya faru da Najeriya."
Kotun ƙararrakin zaɓe: Obi yana ɓata lokacinsa ne kawai in ji malamin addinin Kirista
A rahoton PM News, Giwa ya ƙara da cewa Obi yana ɓata lokacinsa ne kawai, inda ya bayyana shi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na dandalin sada zumunta.
Giwa ya bayyana cewa gaskiya ce ya faɗawa Obi, inda ya ƙara da cewa Ubangiji yana gani ne ba kamar yadda mutum ke gani ba, mutane na duba ne ya zuwa zahiri, a yayin da Ubangiji ke duba ya zuwa zuciya.
Rikici ya sake ɓallewa tsakanin Wike da Atiku
Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan wani sabon rikici da ya sake ɓallewa a tsakanin 'ya'yan babbar jam'iyyar adawa wato PDP, waɗanda suke a rarrabe a gidaje guda biyu.
Rikicin ya biyo bayan goyon bayan wani mamba mai suna Kingsley Chinda, da 'yan Majalisar Wakilai na PDP tsagin Wike, suka marawa baya ya zama shugaban marasa rinjaye a majalisar.
Asali: Legit.ng