Rikicin Cikin Gida Yana Neman Ya Kaure a APC a Kan Kujerun Ministocin Tinubu
- ‘Yan siyasa su na sintiri a fadar Aso Rock Villa musamman tsofaffin Gwamnoni da su ka bar ofis a Mayu
- Babu jituwa tsakanin wasu manya a jam’iyyar APC saboda kowa ya na harin zama Ministan tarayya
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi gum, har yanzu babu wanda zai iya cewa ga inda ya dosa
Abuja - Fafutukar samun kujerar Ministan tarayya a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, ya jawo sabani tsakanin wasu cikin jagororin jam’iyyar APC.
Vanguard ta ce Gwamnoni da tsofaffin gwamnonin jihohi da shugabannin APC su na yaki domin ganin Bola Ahmed Tinubu ya ba su mukamin Minista.
Baya ga wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC, akwai kusoshin jam’iyyun adawa irinsu PDP da NNPP da ke harin Ministoci a gwamnati mai-ci.
Yaushe za a nada Ministoci?
Wasu majiyoyi sun ce sabon shugaban kasar zai aika da sunayen Ministocinsa zuwa majalisa a ranar 4 ga Yuli da Sanatoci za su koma bakin aikinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wani rahoton na dabam, an fahimci za a rantsar da Ministoci ne bayan kammala shari’ar da ake yi a kotu a kan sakamakon zaben shugaban kasa.
A jihohi irinsu Osun, rikici ake yi tsakanin tsohon Ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola da magajinsa Gboyega Oyetola da ya rasa tazarce a 2022.
Sanannan abu ne ba a ga maciji tsakanin magoya bayan Abdullahi Umar Ganduje da Rabiu Kwakwanso wanda yake samun fada wajen shugaban kasa.
'Yan APC ba su so a jawo na waje
Wasu jagororin APC sun huro wuta cewa bai kamata shugaba Tinubu ya nada kowa ba sai cikakkun ‘yan jam’iyya da su taimaka masa a zaben 2023.
‘Yan siyasar su na ganin jawo ‘yan adawa zai zama tamkar kura da shan bugu, gardi da karbar kudi. Sai da hakan zai iya taimakawa APC a siyasance.
Zuwa yanzu masu neman mukamai daga cikin tsofaffin Gwamnoni da sauran ‘yan siyasa sun cika Aso Rock, su na kai takardu domin samun kujera.
Za a iya zuwa da sabon salo
Wata majiya ta tabbatar da cewa ana ta karbar takardun CV na masu harin zama Ministoci, amma har yanzu an rasa gane inda shugaban kasa ya dosa.
A cewar wani na kusa da fadar, babu mamaki masu bada shawarar da aka nada su samu iko sosai a gwamnati, ya zama su ke juya Ministocin da za a nada.
EFCC ta na neman Matawalle?
Kwanaki 21 da su ka wuce kenan da Bello Matawalle ya sauka daga ofis a matsayin Gwamnan Zamfara, sai aka fara jin labari EFCC ta na neman shi.
Ana zargin an karkatar da N70bn ta kwangilolin bogi a jihar Zamfara. Amma hukumar EFCC ta karyata batun, ta ce sam ba ta neman Matawalle.
Asali: Legit.ng