“An Dade Ana Cutarmu”: Yan Asalin Abuja Sun Nemi a Basu Kujerar Minista

“An Dade Ana Cutarmu”: Yan Asalin Abuja Sun Nemi a Basu Kujerar Minista

  • An bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya zabi dan asalin Abuja a matsayin ministan babban birnin tarayya
  • Alhaji Mohammed Yamawo, basarake a Dei-Dei, wani yankin Abuja, ne ya yi rokon
  • Tun bayan samar da mukamin, mutane 16 ne suka riki kujerar ministan kuma ba a taba samun asalin dan yankin ba ko daya

FCT, Abuja - Yan asalin Abuja sun fara yakin neman a mika masu kujerar ministan babban birnin tarayya (FCT) maimakon kawo wani dan waje don ya jagorance su.

Tun bayan kafa mukamin a 1976, ba a taba samun dan asalin Abuja da ya hau kujerar ba.

An dai ta rarraba mukamin ministan Abuja ne a tsakanin ma'aikatan gwamnati 16 daga yankunan kudu maso yamma, arewa maso gaban, arewa maso yamma da arewa ta tsakiya ba.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Tinubu Ya Karbi Bakuncin Mai Kudin Afrika, Aliko Dangote a Aso Rock

Shugaban kasa Bola Tinubu
“An Dade Ana Cutarmu”: Yan Asalin Abuja Sun Nemi a Basu Kujerar Minista Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

A wata hira da Legit.ng ta yi da wasu yan Abuja, masana, sarakuna, jami'an gwamnati sun bayyana matsayinsu kan wannan kira da abun da ya kamata shugaban kasa Bola Tinubu ya yi don ganin mafarkinsu ya zama gaskiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake magana da Legit.ng a wajen kaddamar da rijiyar burtsatse a makarantar firamare ta LEA, Saburi 1, Dei-Dei Abuja, basaraken yankin, Alhaji Mohammed Yamawo, ya ce lokaci ya yi da gwamnatin tarayya za ta saurari kukansu.

Ya bayyana cewa kawo wani dan waje da bai da masaniya kan babban birnin tarayyar zai ci gaba da kawo rashin ci gaba ga asalin mutanen Abuja.

Yamawo ya ce zai yi matukar wahala ga yan waje su fahimci halin da suke ciki saboda su ba yan cikinsu bane.

Kalamansa:

"Muna rokon shugaban kasar Najeriya (Baba Tinubu) da ya duba sannan ya taimaka mana ya yi wani abu a kai sai Allah ya baka lafiya, mulki da shekaru masu yawa don shugabantar kasarmu."

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kotu Ta Ba DSS Sabon Umurni a Kan Godwin Emefiele Da Ke Tsare a Hannunta

Yanzu ne lokacin da ya fi dacewa mu zama minista - Danladi

Hakazalika, shugaban kungiyar PTA na makarantar LEA, Saburi 1, Idris Danladi, ya fada ma Legit.ng cewa babu wani lokaci da ya fi da shugaban kasa Tinubu zai nada dan Abuja a matsayin ministan babban birnin tarayya ba.

Ya ce:

"Yanzu ne lokacin da ya fi dacewa garemu mu zama a kan kujerar ministan babban birnin tarayya saboda an dade ana cutar mutanenmu kuma magana ta gaskiya, abun ya ishemu haka.
"Muna rokon shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya duba wannan a matsayin ci gaba a garemu mu yan babban birnin tarayya. Babu adalci a kawo wani daga waje da bai san abun da ke faruwa a babban birnin tarayya ba."

Da aka tambaye su ko suna kokarin ganin mafarkinsu ya zama gaskiya, Danladi ya ce shugabanninmu da masu ruwa da tsaki a harkar siyasa sun fara kokarin ganin haka.

Kara karanta wannan

Muhammadu Sanusi II Ya Fayyace Dalilan Zuwa Aso Rock da Abin da Ya Fadawa Tinubu

Ambasada Eva Erokoro, mai aikin taimako kuma shugabar gidauniyar Askevena, ta ce ci gaba ne mai kyau idan aka duba yiwuwar ba yan Abuja kujerar ministan babban birnin tarayya.

Har wayau wani dan yankin Abaji mai suna Mallam Abubakar ya ce basu wannan kujera zai taimaka sosai wajen kawo ci gaba ga mutanensu.

"Lallai mun cancanci a bamu wannan kujera ko don goben yaranmu. Ka san ance mai daki shi ya san inda yake yi masa yoyo, sai ka ga ba cin moriyar abubuwa mu da muke yan asalin yankin kamar yadda baki ke ci.
"Ga mu dai an barmu a kauyuka muna fama da noma babu wani ingantaccen ilimi mai nagarta. Muna kira ga shugaban kasa ya duba kokenmu."

Asalin yan Abuja sun kasance Gwarawa wanda aka fi sani da Gwari kuma Gwaranci shine yaren da aka fi yi a yankin.

Shugaban kasa Tinubu ya nada ministoci 27? gaskiya ta bayyana

Kara karanta wannan

“Ba Zan Iya Rayuwa Babu Ita Ba”: Dan Najeriya Ya Yi Wuff Da Tsohuwar Baturiya, Hotunan Su Yadu

A wani labarin, mun ji cewa an gano cewa jerin sunayen sabbin nade-nade 27 da wasu sabbin ma'aikatu da ake zargin shugaban kasa Bola Tinubu ya samar kuma suka karade Facebook na bogi ne.

Kamar yadda Africa Check, wani dandamalin binciken kwakwaf ya rahoto, ana ta yada jerin sunayen mutanen 27 wanda aka tabbatar da karya ne, a shafukan Facebook, tare da ikirarin cewa shugaban kasa Tinubu ya soke wasu kujerun ministoci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng