Jigon APC Ya Bayyana Hukuncin Da Ya Dace PDP Ta Yi Wa Wike Bisa Cin Amanarta Da Atiku
- Jigon jam'iyyar APC ya bayyana abinda yakamata jam'iyyar PDP ta yi wa tsohon gwamna Nyesom Wike bayan hukuncin da kotu ta yi kwanan nan
- Da yake magana kan hukuncin babbar kotu na goyon bayan dakatar da Wike daga PDP, Eze Chukwuemeka Eze ya ce yakamata PDP ta kori Wike
- Eze, ya ƙara da cewa irinsu Wike bayan abinda ya yi wa Atiku Abubakar a zaɓen da wuce bai kamata a lallaɓa su ba, kora suka cancanci samu
Port Harcourt, jihar Rivers - Wani babban jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Eze Chukwuemeka Eze, ya bayyana abinda yakamata jam'iyyar adawa ta PDP ta yi wa waɗanda suka ci amanarta da dunduniyar ɗan takararta a zaɓen da ya gabata.
Jigon na jam'iyyar APC ya yaba da hukuncin babbar kotun tarayya wanda ya ce jam'iyyar PDP tana da ƴancin dakatar da tsohon gwamnna jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike, daga jam'iyyar.
Jigon APC ya goyi bayan hukuncin kotu na umartar PDP ta dakatar da Wike
Eze a ranar Juma'a 16 ga watan Yuni, ya bayyana cewa hukuncin, ya wanke shawarar da ya ba PDP kafin zaɓen 2023, inda ya shawarci jam'iyyar da ta gaggauta korar Wike daga cikinta, wanda ake zargin ya kitsa yadda Atiku Abubakar zai sha kashi a zaɓen.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya yi nuni da cewa tun da hukuncin kotu ya goyi bayan PDP, jam'iyyar har yanzu tana da sauran damar korar irinsu Wike sannan ta fara ƙoƙarin farfaɗowa daga asarar da ta tafka, cewar rahoton Leadership.
Jigon na APC ya bayyana cewa yana goyon bayan hakan ne saboda ƙasar nan na buƙatar jam'iyyun adawa masu ƙarfi waɗanda za su riƙa sanya idanu kan shirye-shiryen gwamnati domin kare muradun ƴan Najeriya.
Wike Ya Yaba Wa Shugaba Tinubu
A wani labarin na daban kuma, tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya yaba wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Wike ys ce dakatar da Emefiele abu ne mai kyau wanda kuma aka gudanar akan lokacin da ya dace.
Asali: Legit.ng