Hukumar EFCC Ba Ta Taba Gayyata Na Ba, Tsohon Shugaban Kasa Jonathan
- Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya ƙaryata kalaman wani mawaƙi cewa EFCC ta gayyace shi bayan ya bar mataimakin gwamna a Baylesa
- A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Wealth Dickson Ominabo, ya fitar ranar Jumu'a, Jonathan ya ce ƙarya ake masa
- A zamanin mulkin Muhammadu Buhari, EFCC ta gurfanar da mukarraban Jonathan da Ministocinsa da dama a gaban Kotu
Bayelsa - Tsohon shugaban kasa, Dakta Goodluck Ebele Jonathan, ya karyata ikirarin wani mawaƙi cewa hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta taɓa gayyatarsa.
Fitaccen mawakin mai suna, Femi Kuti, ya yi zargin cewa EFCC ta taɓa gayyatar Jonathan domin ya amsa wasu tambayoyi kan ɓatan wasu kuɗaɗe.
A cewar Mawaƙin hukumar ta titsiye Jonathan bisa zargin zambar kuɗaɗe bayan ya sauka daga matsayin mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.
Menene gaskiyar ikirarin da mawaƙin ya yi kan Jonathan?
Bayan wannan zargin da mawaƙin ya jefa wa Jonathan, tsohon shugaban ƙasa ya ce sam ba haka bane kuma kalaman da ya faɗa duk ƙaryane, rahoton Punch ya tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai magana da yawun tsohon shugaban ƙasa, Wealth Dickson Ominabo, shi ne ya musanta zargin a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a, 16 ga watan Yuni, 2023.
Ya bayyana cewa mai yuwuwa wasu labaran ƙarya da wasu gurɓatattun 'yan siyasa suka kirkira kuma suka jingina wa Jonathan ne suka ruɗi Kuti ya yi wannan ikirarin.
Kakakin Jonathan ɗin ya kara da jaddada cewa hukumar EFCC da kanta ta ba da shaida mai tsafka kan tsohon shugaban ƙasa a wannan lokacin da Kuti ke magana a kai.
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa duk da bata gayyaci Jonathan ba, EFCC ta tsitsiye da yawa daga cikin muƙarrabansa da Ministoci bisa zargin wawure kuɗin baitulmali.
Shugaba Tinubu Ya Kafa Tarihi, Ya Kara Motocin Kashe Gobara a Ayarin motocin shugaban ƙasa
A wani rahoton na daban kuma Shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya amince da sanya motocin kashe gobara a cikin ayarin tawagar shugahan ƙasa.
Shugaban hukumar kwana-kwana ta ƙasa (FFS), Abdulganiyu Jaji, ya ce wannan ne karon farko da shugaban ƙasa ya yi haka a tarihin Najeriya.
Asali: Legit.ng