Gwamnan Kano, Abba Gida Gida, Ya Mayar Da Shugaban Hukumar Haraji Da Ganduje Ya Cire Kan Muƙaminsa

Gwamnan Kano, Abba Gida Gida, Ya Mayar Da Shugaban Hukumar Haraji Da Ganduje Ya Cire Kan Muƙaminsa

  • Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya mayar da tsohon shugaban Hukumar Tattara Haraji ta jihar Kano (KIRS), Alhaji Sani Abdulkadir Dambo, bakin aiki
  • Tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ne ya kori Dambo a shekarar 2021 bisa zargin cin hanci da rashawa
  • Abba ya kuma naɗa Alhaji Isyaku Abdullahi Kubarachi, a matsayin Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA)

Kano Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mayar da tsohon shugaban Hukumar Tattara Haraji ta jihar Kano (KIRS), Alhaji Sani Abdulkadir Dambo, wanda tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kora daga aiki kan mukaminsa.

Hakan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Sanusi Dawakin Tofa ya fitar a ranar Juma’a, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida: Sabon Gwamna Ya Sake Fito da Tsarin Zuwa Jami’o’in Kasashen Waje

Biyo bayan zargin cin hanci da rashawa, gwamnatin Ganduje ta dakatar da Dambo tare da umartar manajan daraktan kamfanin kayayyakin gona na jihar Kano (KASCO), da ya karɓi ragamar hukumar har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

Abba ya maida tsohon shugaban Hukumar Tattara Haraji ta jihar Kano kan muƙaminsa
Gwamnan Kano, Abba Gida-Gida ya maido da Alhaji Sani Abdulkadir Dambo kan muƙaminsa. Hoto: Freedom Radio Nigeria
Asali: UGC

Tarihin aikin sabon shugaban hukumar harajin

A yanzu haka Dambo babban manaja ne a Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa (FIRS) a Abuja.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kammala karatunsa na lissafin kuɗi a Jami’ar Bayero da ke Kano inda ya yi digiri na biyu a fannin lissafi da gudanar da kuɗi, da kuma digiri na biyu a ɓangaren gudanar da kasuwanci (MBA).

Shugaban hukumar tattara kuɗaɗen shigar da aka dawo da shi, mamba ne a cibiyar kula da haraji ta Najeriya, kuma yana da gogewar shekaru 20 a kan harkokin karɓar haraji.

Gwamnan ya buƙaci Dambo ya fara aiki nan take

Kara karanta wannan

Gudaji Kazaure Ya Lissafa Jerin Sunayen Ministoci Da Muƙarraban Buhari Da Ya Kamata Tinubu Ya Kama Su Da Dalilai, Bidiyon Ya Yadu

Gwamnan ya kuma amince da naɗin Alhaji Isyaku Abdullahi Kubarachi, a matsayin babban sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta jihar Kano (SEMA).

Sanarwar ta kara da cewa naɗin da aka yi wa mutanen biyu ya fara aiki nan take, inda ake sa ran za su fara aiki a yau Juma'a 16 ga watan Yuni 2023.

Abba Gida Gida ya yi magana kan dawo da Sanusi Lamido kujerarsa

A wani labarin da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun karanta cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi magana kan batun dawo da tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi Lamido Sanusi II kan kujerar sarautarsa da Ganduje ya cire shi.

Abba ya ce har yanzu bai gama yanke shawara ba kan batun maido da tsohon sarkin kan muƙaminsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng