Tazarce Karo Na Uku: Obasanjo Ya Bayyana Masu Son Ya Yi Tazarce, Ya Bayyana Dalilansu
- Tsohon shugaban ƙasa Obasanjo ya yi magana kan ƙoƙarin yi wa kundin tsarin mulkin shekarar 1999 kwaskwarima domin ya yi tazarce karo na uku
- Obasanjo ya bayyana cewa wasu gwamnonin jihohi a lokacin a shekarar 2006 sun yi na'am da wannan ƙudirin tazarcen nasa
- A cewar tsohon shugaban ƙasan, gwamnonin suna son tazarcen karo na uku ne saboda za su samu damar yin hakan a jihohi
Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi magana kan tazarcen da ya so ya yi karo na uku wanda bai yi nasara ba lokacin yana kan mulkin ƙasar nan a karo na biyu.
Idan ba a manta ba a shekarar 2006, an kai wani kuɗiri gaban majalisar tarayya domin yi wa kundin tsarin mulkin shekarar 1999 gyara da ƙara wa'adin mulki, ƙudirin da aka ƙi amincewa da shi.
Obasanjo ya bayyana cewa akwai hannun wasu gwamnonin jihohi a cikin tazarcen karo na uku saboda suna son su yi hakan a jihohinsu, rahoton The Cable ya tabbatar.
Da yake magana a yayin tattaunawa da wani gogaggen ɗan jarida, Chude Jideonwo, tsohon shugaban ƙasar ya bayyana cewa wasu gwamnonin sun so ƙara wa'adin mulkinsu da shekara huɗu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da yake magana kan tazarcen nasa wanda bai yiwu ba, Obasanjo ya bayyana cewa:
“Gwamnonin, wasu daga cikinsu saboda kansu su ke yi."
"Saboda idan shugaban ƙasa ya yi mulki a karo na uku, su ma za su samu damar yin mulki sau uku."
Ya musanta salwantar da dukiyar ƙasa
Da yake magana kan zarge-zargen salwantar da dukiyar ƙasa da ake masa, Obasanjo ya bayyana cewa ya ƙware ne a wajen samar da kuɗi ba salwantar da su ba.
Ya bayyana cewa mutanen da ba za su iya yin abubuwan da ya yi ba, su daina sukar shi.
Lokacin Shugaban Kasa Mace Ya Yi a Najeriya - Obasanjo
A wani labarin na daban kuma, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa lokaci ya yi da yakamata ƙasar nan ta samu shugaba mace.
Tsohon shugaban ƙasar ya yi kiran da a miƙa ragamar mulkin ƙasar nan a hannun mata domin a jaraba kamun ludayinsu.
Asali: Legit.ng