Dan Majalisa A Bauchi, Ado Wakili, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Kwanaki 3 Kafin Wa'adinsa Ya Kare

Dan Majalisa A Bauchi, Ado Wakili, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Kwanaki 3 Kafin Wa'adinsa Ya Kare

  • An yi babban rashi yayin da dan majalisa mai wakiltar mazabar Burra da ke cikin jihar Bauchi ya rasu kwanaki uku kafin wa'adinsa ya kare
  • Marigayin, Honarabul Ado Wakili bai samu damar komawa kujerarsa ba bayan da ya sha kaye a zaben da aka gudanar a watan Maris
  • Kakakain majalisar jihar, Honarabul Abubakar Y Sulaiman ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai saukin kai da fara'a

Jihar Bauchi - Dan majalisar dokokin jihar Bauchi, Honarabul Ado Wakili ya riga mu gidan gaskiya.

Ado Wakili kafin rasuwarsa, shi ne ya wakilci mazabar Burra, yayin da ake saura kwana uku wa'adinsa ya kare.

Marigayi Ado Wakili da ya rasu a jihar Bauchi
Marigayi Dan Majalisar Jihar Bauchi, Ado Wakili. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Marigayin bai samu damar komawa kujerarsa ba yayin da ya sha kaye a zaben da aka gudanar a watan Maris, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Jerin Manyan Jami’an Gwamnati 1 Da Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Cikin Makonni 2

Da yake sanar da rasuwar, kakakin majalisar jihar Honarabul Abubakar Y Sulaiman ya bayyana kaduwarsa da jin rasuwar Wakili.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana Wakili a matsayin dan uwa kuma dattijo wanda suke dauka kamar uba ga dukkan'yan majalisar, Daily Post ta tattaro.

Ya kara da cewa, Wakili mutum ne mai kima da kankan da kai, ga kuma fara'a duk da yawan shekarunsa amma ya dauki kowa a majalisar kamar abokinsa.

A cewarsa:

"Mun yi rashin uba kuma dan uwa wanda yanzu mazabarsa da majalisar, da ma jihar baki daya ke bukatar gudumawarsa.
"A madadin 'yan majalisar da sauran ma'aikata muna mika sakon ta'aziya ga iyalansa da al'ummar mazabar Burra da ma karamar hukumar Ningi bisa wannan babban rashi.
"Muna addu'ar Allah ya gafarta masa yasa Aljanna Firdausi ce makomarsa.

Tuni aka yi sallar jana'izarsa da misalin karfe 1:30 na rana a yau Juma'a 16 ga watan Yuni a masallacin Gwallaga da ke cikin Bauchi.

Kara karanta wannan

“Rashawa Kiri-Kiri”: Babban Lauya Ya Caccaki Tsohon Sanata Kan Sakin Bakin Da Ya Yi a Zauren Majalisar Dattawa

Yan Daba Sun Sari Dalibin Jami'a a Jihar Bauchi Kan Gardamar Kwallon Kafa

A wani labarin, tsagera sun sari dalibin jami'ar Sa'adu Zungur mai suna Safiyanu Adamu a jihar Bauchi.

An samu hatsaniya a dalilin kwallon kafa tsakanin Green House da GT House a ranar Asabar.

Yayin da daya daga cikin daliban suka samu hargitsi inda dan daban ya caka masa wuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.