Cikakken Jerin Ministocin da Ake Tsammanin Tinubu Zai Nada Gabanin 28 Ga Yuli
Tun daga ranar da ya karbi mulkin Najeriya, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya fara iki ba kama hannun yaro kuma ya jure wa duk wata matsin lamba da ta biyo bayan wasu matakan da ya ɗauka.
Ayyukan da shugaba Tinubu ya fara yi daga shiga ofis ya sa 'yan Najeriya suka ƙara ɗora tsammani kan sabon shugabansu kuma tuni aka fara zancen su wa zai naɗa Ministoci, The Cable ta ruwaito.
Meyasa ya zama wajibi Tinubu ya gabatar da sunayen Ministoci gabanin ranar 28 ga watan Yuli, 2023?
A halin yanzun, shugaba Tinubu ba zai tsaya iya nan ba kuma ana tsammanin zai fitar da jerin sunayen Minstocinsa daga nan zuwa ranar 28 ga watan Yuli, 2023, saboda daga ranar ya cika watanni 2 a Ofis.
Sabuwar dokar da tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya rattaɓa wa hannu ta nuna duk sabon shugaban da ya zo, yana da watanni 2, watau kwanaki 60 ya miƙa sunayen ministoci ga majalisa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Matukar Tinubu bai yi wa wannan doka garambawul ba, ana ganin zai miƙa sunayen Ministoci 27 daga yanzu zuwa ranar 28 ga watan Yuli mai zuwa.
Jerin ministocin da Shugaba Tinubu zai naɗa
1. Ministan birnin tarayya Abuja
2. Ministan noma da raya karkara
3. Ministan harkokin sufurin jiragen sama a Najeriya
4. Ministan Kasafin kudi da tsare-tsaren ƙasa
5. Ministan kasuwanci da masana'antu
6. Ministan ilimi
7. Ministan mahalli
8. Ministan kuɗi
9. Ministan lafiya
10. Ministan yaɗa labarai da al'adu
11. Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani
12. Ministan harkokin cikin gida
13. Ministan shari'a
14. Ministan kwadugo da samar da ayyukan yi
15. Ministan albarkatun man fetur
16. Ministan albarkatun ruwa
17. Ministan harkokin mata da walwala
18. Ministan ma'adanan ƙasa da ƙarafa
19. Ministan tsaro
20. Ministan Neja Delta
21. Ministan wutar lantarƙi
22. Ministan sufuri
23. Ministan ayyukan jin ƙai, Ibtila'i da walwalar al'umma
24. Ministan kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire
25. Ministan matasa da wasanni
26. Ministan ayyuka da gidaje
27. Ministan harkokin waje.
Idan baku manta ba a makon da ya shiga, shugaba Tinubu ya tura wasiƙa ga majalisar dattawa, yana neman ta sahale masa ya naɗa masu ba da shawara 20.
Jerin Jihohin da Shugaba Tinubu Zai Gamu da Ciwon Kai Yayin Zaɓo Ministoci da Dalilai
A wani labarin kuma mun kawo muku jerin sunayen jihohin da shugaba Tinubu zai iya fama wajen zaɓo wanda zai naɗa a matsayin minista.
Mafi karanci, ana hasashen shugaban ƙasan zai sha wahala wajen zaɓo Ministoci a jihohi 4 saboda jam'iyyar APC ta sha kashi a zaben gwamna da Sanatoci a jihohin.
Asali: Legit.ng