Jerin Jihohin da Shugaba Tinubu Zai Gamu da Ciwon Kai Yayin Zaɓo Minista da Dalilai
Jam'iyyar APC a matakin jihohi a yanzu tana dakon umarnin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, cewa ta miƙa sunayen waɗanda za'a naɗa Ministoci ga uwar jam'iya ta ƙasa.
Bayan miƙa sunayen ga hedkwatar jam'iyya mai mulki ta ƙasa ne ake tsammanin zasu isa ga fadar shugaban ƙasa domin tantancewa da kuma naɗa su a cikin muƙarrabai.
Punch ta tattaro cewa alamu sun nuna shugaba Tinubu ka iya gamuwa da ciwan kai wajen zaɓo Ministoci daga wasu jihohin saboda yadda ta kaya a sakamakon zaben 2023 a jihohin.
Mafi karanci, ana hasashen shugaban ƙasan zai sha wahala wajen zaɓo Ministoci a jihohi 4 saboda jam'iyyar APC ta sha kashi a zaben gwamna da Sanatoci a jihohin.
Legit.ng Hausa ta haɗo muku jihohin, ga su kamar haka;
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
1. Jihar Delta
Rahoton Punch ya yi ikirarin cewa da farko mafi akasarin mambobin APC sun amince Festus Keyamo, tsohon ƙaramin Ministan kwadugo da ayyukan yi ya shiga jerin hadiman Tinubu.
A halin yanzu bayan APC ta sha kashi a zaben gwamna, sunan tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, ya shiga cikin waɗanda ake ganin za'a miƙa daga jihar.
2. Jihar Osun
Gabanin Kotun koli ta yanke hukunci wanda ya tabbatar da nasarar PDP a zaɓen gwamnan jihar Osun, tsohon ministan lafiya, Farfesa Isaac Adewole, za'a miƙa wa Tinubu.
Amma bayan hukuncin Kotun koli, da yawan mambobin APC sun koma bayan tsohon gwamna, Gboyega Oyetola, a matsayin wanda ya fi cancanta da zama Minista.
3. Jihar Ekiti
An gano cewa shugabannin APC a matakin ƙasa suna kokarin kamun kafa da bin matakai domin ganin Dayo Adeyeye, wanda ya jagoranci kamfen Tinubu a Kudu maso Yamma, ya ɗare kujerar Minista.
A bangaren APC reshen jihar Ekiti kuma tana ganin tsohon gwamna, Kayode Fayemi, ne ya fi dacewa sunansa ya shiga cikin jerin Ministocin shugaban ƙasa.
4. Jihar Zamfara
Da akwai makamancin wannan matsala a Zamfara da ke Arewa maso yammacin Najeriya, inda ake ganin shugaba Tinubu zai gamu da ciwon kai wajen zaɓo ɗaya daga cikin jiga-jigai 2.
Jaridar da tattaro cewa mutum biyun da shugabn kasa zai la'akari kuma ya ɗauki ɗaya sun haɗa da tsohon gwamna, Bello Matawalle, da Sanata Kabir Marafa.
Yakasai da Bisi Akande Sun Gana da Shugaba Tinubu a Aso Rock
A wani rahoton na daban Alhaji Tanko Yakasai da Bisi Akande sun ziyarci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a fadarsa da ke Abuja ranar Alhamis.
Manyan jiga-jigan sun yaba da kamun ludayin sabon shugaban ƙasan, inda aka ji suna cewa 'yan Najeriya suna murna da samun shugaba.
Asali: Legit.ng