Shugaba Tinubu Ya Nada Ribadu, Darazu, Alake da Wasu 5 a Matsayin Mashawarta

Shugaba Tinubu Ya Nada Ribadu, Darazu, Alake da Wasu 5 a Matsayin Mashawarta

  • Shugaban Najeriya, Alhaji Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗa mutane 8 a matsayin ma su ba da shawara ta musamman
  • A wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban ƙasa, Tinubu ya naɗa Nuhu Ribaɗo, Ya'u Darazo da wasu jiga-jigai a muƙamai daban-daban
  • Wannan na zuwa ne awanni kaɗan bayan shugaban ƙasa ya dakatar da shugaban hukumar EFCC, Bawa kuma ya umarci a gudanar da bincike a kansa

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗa sabbin mashawarta na musamman guda 8, kamar yadda rahoton Daily Trust ya kawo.

Wannan naɗe-naɗe na kunshe ne a wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na fadar shugaban ƙasa, Abiodun Oladunjoye, ya fitar ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Nada Ribadu, Darazu, Alake da Wasu 5 a Matsayin Mashawarta Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jerin sunaye da muƙaman da Tinubu ya naɗa mutane 8

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule Da Abdulsalam Abubakar a Villa, Bayanai Sun Fito

A cewar sanarwan, sabbin masu bai wa shugaban ƙasa shawaran sun haɗa da;

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. Mista Dele Alake a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru.

2. Ya'u Darazo a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan harkokin siyasa da gwamnatoci.

3. Mista Wale Edun a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan tsare-tsaren kuɗi.

4. Malam Nuhu Ribaɗo a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan harkokin tsaro.

5. Misis Olu Verheijen a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan makamashi.

6. Mista Zachaeus Adedeji a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan tattara haraji.

7. Mista John Ugochukwu Uwajumogu, mai ba da shawara ta musamman kan masana'antu, kasuwanci da hannayen jari.

8. Salma Ibrahim Anas, wacce zata riƙe ofishin mai ba da shawara ta musamman kan harkokin lafiya.

Kara karanta wannan

Abubuwa 4 Da Ake Ganin Suna Da Alaka Da Dakatar Da Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa Da Tinubu Ya Yi

Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa

A wani rahoton na daban kuma shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar EFCC na ƙasa har sai baba ta gani.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Willie Bassey, daraktan labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya ya saki a ranar Laraba, 14 ga watan Yuni, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262