Tinubu Zai Duba Yiwuwar Tsawaita Wa'adin Dena Amfani Da Tsaffin Naira A Najeriya

Tinubu Zai Duba Yiwuwar Tsawaita Wa'adin Dena Amfani Da Tsaffin Naira A Najeriya

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na duba yiwuwar tsawaita wa’adin kashe tsofaffin takardun kuɗaɗen Najeriya da aka sanya
  • A kwanakin baya ne kotun ƙoli ta ɗage wa'adin amfani da tsoffin takardun kuɗin na naira da aka sanya, zuwa watan Disamban shekarar 2023
  • Wani kwamitin shawarar na Shugaba Bola Tinubu, na duba yiwuwar tsawaita wa’adin amfani da na tsofaffin takardun kuɗin na naira zuwa watan Disamban 2024

Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na duba yiwuwar tsawaita wa’adin kashe tsofaffin takardun kuɗin Najeriya.

A shekarar da ta gabata ne babban bankin Najeriya (CBN), ya sake fasalin kuɗaɗen Najeriya sannan ya sanya wa'adi ga tsoffin, wanda aka tsawaita bayan an kai ruwa rana.

Sai dai a hukuncin da kotun ƙoli ta yanke kan ƙarar da wasu gwamnonin suka shigar, ta ɗage wa'adin kashe tsofaffin kuɗaɗen har zuwa watan Disamban 2023.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Bayyana Lokacin da Za'a Fara Bai Wa Ɗaliban Najeriya Bashin Kuɗi

Tinubu zai duba batun wa'adin amfani da tsofaffin takardun kuɗaɗe
Akwai yiwuwar Tinubu ya tsawaita wa'adin amfani da tsoffin takardun kuɗi. Hoto: Anadolu Agency
Asali: Getty Images

Kwamitin shawarwari na Tinubu ya bukaci a tsawaita wa'adin zuwa 2024

Sai dai a wani rahoto da Daily Trust ta wallafa, kwamitin shawara na shugaban ƙasa Bola Tinubu, ƙarƙashin jagorancin Sanata Tokunbo Abiru, ya buƙaci a ƙara wa’adin zuwa watan Disamba na 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tokunbo Abiru, ya kasance tsohon babban jami’in bankin Polaris kafin a zaɓe shi a matsayin sanata mai wakiltar Legas ta gabas, bayan rasuwar Sanata Gbenga Oshinowo, da ya gabace shi.

Haka kuma a cikin kwamitin akwai Dokta Yemi Cardoso, wani babban aminin shugaban ƙasa, wanda ya taka muhimmiyar rawa a lokacin da Tinubu yake gwamnan jihar Legas.

Tinubu na da ƙudurin neman mulki wa'adi na biyu

Rahoton shawarar ya kuma bayyana irin nasarorin da gwamnatin mai ci ke son cimmawa cikin shekaru 8 masu zuwa, hakan ya bayyana shirin Tinubu na neman wa'adi na biyu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya Ta Bayyana Rukunin Mutane 5 Da Ta Haramtawa Amfana Da Rancen Kuɗin Karatun Dalibai

A halin da ake ciki, Shugaba Tinubu na da wa'adin shekaru 4 ne kawai, bayan zaɓarsa da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairun, 2023.

A cikin shawarwarin akwai burin haɓaka tattalin arzikin zuwa dala tiriliyan 1, wanda ake sa ran zai fidda sama da mutum miliyan 100 daga ƙangin talauci.

Tinubu na cikin waɗanda suka tursasawa gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari tsawaita wa'adin kashe tsofaffin takardun kuɗaɗen a can baya.

Abubuwan da ake ganin sun jawo dakatar da shugaban EFCC da Tinubu ya yi

A wani labarin da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun karanta wasu dalilai da ake ganin suna da alaƙa da dakatarwar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa.

Da yammacin ranar Laraba ne dai aka samu labarin dakatar da Abdulrasheed Bawa daga shugabancin hukumar ta EFCC, gami da umartarsa da ya miƙa ragamar shugabancin ga daraktan ayyuka na hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng