A Jira Lokaci: Abba Gida Gida Ya Magantu Kan Dawo da Korarren Sarki Sanusi, Ya Fadi Shirinsa

A Jira Lokaci: Abba Gida Gida Ya Magantu Kan Dawo da Korarren Sarki Sanusi, Ya Fadi Shirinsa

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce bai yanke shawara akan makomar sabbin masarautun jihar ba kamar yadda ake yadawa
  • Gwamnan ya bayyana haka ne ganin yadda jita-jita ke yawo a garin cewa yana so ya dawo da tsohon sarkin Kano Sunusi Lamido Sunusi
  • Abba ya bayyana haka ne a ranar Laraba 14 ga watan Yuni ta bakin sakataren yada labarai Sanusi Bature inda ya ce jita-jita ce kawai

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce har yanzu bai yanke shawara akan sauya masarautun jihar ba kamar yadda ake yadawa.

Gwamnan ya bayyana haka ne bayan jita-jita ta cika gari cewa zai wargaza masarautun da tsohon gwamna Ganduje ya yi da kuma dawo da Sunusi Lamido Sunusi kan kujerar sarautar birnin Kano.

Kara karanta wannan

“Rashawa Kiri-Kiri”: Babban Lauya Ya Caccaki Tsohon Sanata Kan Sakin Bakin Da Ya Yi a Zauren Majalisar Dattawa

Abba ya ce bai shirya dawo da Sunusi kan mulki ba
Abba Gida Gida Da Tsohon Sarkin Kano, Sunusi Lamido. Hoto: The Daily Reality.
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Laraba 14 ga watan Yuni ta bakin sakataren yada labarai Sanusi Bature inda ya tabbatar da cewa wannan jita-jita ce kawai.

Gwamnan ya ce bai yanke shawarar akan sabbbin masarautun Kano ba

A cewar sanarwar:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sabanin abin da ke yawo a kafar sadarwa, gwamnatin Kano har yanzu ba ta yanke shawara akan sabbin masarautun jihar ba.

Bature ya ce za a ba wa 'yan Kano damar sanin duk abin da ke faruwa tsakanin gwamnatin jihar da 'yan majalisar jihar akan duk wata babbar doka da gwamnatin za ta gabatar.

Ya ce abin da ya wakana tsakanin gwamnatin jihar da majalisar jihar kawai shi ne amincewa bukatar gwamnan jihar da suka yi na nada hadimai na gwamnan da suka amince da ita a ranar Laraba 14 ga watan Yuni.

A cewarsa:

Kara karanta wannan

Sai Na Ga Bayanku: Sabon Gwamnan APC a Arewa Ya Yi Babban Tanadin Karar Da ’Yan Bindiga

"Muna sa ran za a tura sunayen kwamishinoni majalisa a mako mai zuwa don tantance su.

Daily Trust tattaro cewa tun bayan nasarar da gwamnatin Abba Gida Gida ta yi ake ta jita-jitar cewa sabuwar gwamnatin za ta wargatsa tsarin sarautar jihar.

An jiyo Kwankwaso a baya na cewa ya kamata Abba Kabir ya duba yiyuwar dawo da Sunusi

Batun sauya sarautar ya kara yaduwa bayan tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso a wata hirarsa ya ke cewa ya kamata sabuwar gwamnatin yaronsa Abba Gida Gida ta duba yiwuwar sauya sabbin masarautun.

Tun bayan karbar rantsuwar kama mulki a ranar 29 ga watan Mayu, Abba Kabir ya ke ta rushe-rushen wasu gine-gine da ya ce ba gina su bisa tsari ba ko kuma an bayar da su ba ta hanyar da ya dace ba.

Wannan shi yake kara tabbatar da cewa zai iya yiyuwa gwamnatin jihar ta waiwaici sabbin masarautun da ake magana, cewar rahotanni.

Kara karanta wannan

Ranar Damokradiyya: Shehu Sani Ya Saki Jerin Sunayen Yan Arewa Da Suka Yi Fafutukar June 12

Majalisar Jihar Kano Ta Amince da Bukatar Abba Kabir Nada Hadimai 20

A wani labarin, majalisar dokokin jihar Kano ta amince da bukatar gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf na nada hadimai 20.

Hakan ya biyo bayan kudirin da mataimakin kakakin mjalisar, Muhammad Butu ya gabatar a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel