G5: Yadda Jagororin PDP Su Ka Yi Watsi da Jam’iyyarsu, Su Ka Bi APC a Zaben Majalisa
- Nyesom Wike ya ce duka ‘yan tafiyarsu ta G5 sun goyi bayan Godswill Akpabio da Tajudeen Abbas
- Tsohon Gwamnan Ribas ya fadi dalilinsu na goyon bayan ‘Yan APC alhali su na jam’iyyar PDP
- Wike ya ba sababbin shugabannin majalisar shawarar su hada-kai da shugaban kasa, Bola Tinubu
Abuja - Tsohon Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya shaida cewa ‘yan kungiyarsu ta G5, sun goyi bayan Godswill Akpabio da Tajudeen Abbas.
Rahoto ya fito daga tashar talabijin Channels, a nan aka ji Nyesom Wike ya na bayanin yadda shi da sauran ‘yan tawaye su ka hada-kai da APC.
Godswill Akpabio da Tajudeen Abbas ne su ka zama sababbin shugaban majalisar dattawa da wakilai bayan zaben da aka shirya a farkon mako.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An samu hadin-kai a Najeriya
Da ya zanta da manema labarai a garin Fatakawal a ranar Laraba, tsohon Gwamna Wike ya ce samun nasarar Akpabio ya nuna akwai hadin-kai a kasa.
Sanata Akpabio wanda ya zama shugaban majalisar dattawa, ya fito ne daga Kudu maso kudu.
A cewar ‘dan siyasar, sakamakon zaben majalisar ya tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu ba zai bari a raba kan al’umma ba, zai hada-kan Najeriya.
A bi Yarima - a sha kida
Tashar ta rahoto Wike ya na bayyana Akpabio a matsayin kwararre wanda ya san aiki, ya kuma ce majalisarsa ba za ta zama ‘yar amshin shata ba.
"Ba na tunanin Akpabio zai zama ‘dan amshin shata. Na kuma goyi bayan shi domin shi ma ya mara mani baya da na ke neman takarar Gwamna.
Akpabio ya cancanta, ya dace, mutum ne mai ilmi. Ya iya magana kuma zai iya wakiltar kasar nan a ko ina. Wace cancanta kuma ake nema?
- Nyesom Wike
G5 ta taka rawar gani a Majalisa
Vanguard ta ce jigon na PDP ya ce shi da ‘Yan G5 duka sun ba tsohon Gwamnan na Akwa Ibom gudumuwa, ya ce kishin kasa aka sa gaba da jam’iyyar siyasa.
Wike ya yi kira ga Akpabio da Abbas su guji fada da shugaban kasa, ya ce rikici dabam da ‘yanci.
Abokan tafiyarsa su ne Gwamna Seyi Makinde da kuma tsofaffin Gwamnoni: Samuel Ortom (Benue), Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu) da Okezie Ikpeazu (Abia).
Tinubu ya tuna da Abiola
A baya an samu labari cewa Bola Tinubu ya ce janye farashin tallafin fetur ya zama dole, a madadin haka ya sha alwashin gyara wuta, ilmi da asibitoci.
Sabon shugaban kasar ya yabi gwagwarmyar MKO Abiola da mai dakinsa da Janar Shehu Yar’Adua a jawabin da ya gabatar na ranar 12 ga watan Yuni.
Asali: Legit.ng