Akpabio Ya Nemi Muhimman Bukatu Guda 2 Wurin Tinubu Bayan Zama Shugaban Majalisar Dattawa Na 10

Akpabio Ya Nemi Muhimman Bukatu Guda 2 Wurin Tinubu Bayan Zama Shugaban Majalisar Dattawa Na 10

  • Shugaban Majalisar Dattawa na 10, Godswill Akpabio, ya gabatar da wasu muhimman buƙatu guda 2 ga Shugaba Bola Tinubu a lokacin da yake gabatar da jawabin godiya
  • Akpabio ya samu nasarar zama shugaban Majalisar Dattawa bayan kamfen da wasu daga cikin sanatoci, gwamnoni da shugabannin jam’iyyar suka yi masa
  • Tun a farko dai shugaban ƙasa Bola Tinubu, da jiga-jigan jam’iyyar APC, sun bayyana Akpabio a matsayin wanda suke so ya zama shugaban Majalisar Dattawan

FCT, Abuja - Godswill Akpabio, wanda yayi wa'adi biyu a matsayin gwamnan jihar Akwa Ibom, kuma tsohon ministan Neja Delta a ƙarƙashin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya zama shugaban Majalisar Dattawan Najeriya na 10.

Sabon shugaban Majalisar Dattawan ya samu nasara ne ta hanyar neman goyon bayan takwarorinsa sanatoci, kai wa gwamnonin APC ziyara, da ma wasu daga cikin 'yan jam’iyyun adawa.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Sa Labule da Sabon Shugaban Majalisar Dattawa, Gwamnoni 2 da Ganduje, Bayanai Sun Fito

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya nemi haɗin kan Shugaba Tinubu
Akpabio ya roƙi gwamnatin Tinubu ta riƙa gabatar da kasafin kuɗi da wuri. Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Da yake jawabin godiya, sabon shugaban Majalisar Dattawan, ya gabatar da muhimman buƙatu guda 2 ga Shugaba Bola Tinubu, buƙatun sune kamar haka:

Gabatar da kasafin kudi akan lokaci

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya tabbatar da cewa ɓangaren zartaswa yana gabatar da kasafin kudin shekara a kan lokaci don samun ɗorewar da’irar kasafin Kuɗin Janairu zuwa Disamba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Akpabio ya yi wannan tsokaci ne a yayin da yake yabawa Majalisar Dattawa ta 9, kan yadda ta riƙa zartar da kasafin kuɗi a kan lokaci ba kamar yadda Majalisar Dattawa ta 8 da Bukola Saraki ya jagoranta ta riƙa yi ba.

Shugaban majalisar ya kuma yabawa abokin aikinsa kuma tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan, bisa yadda ya riƙa zartar da kasafin kuɗin a kan lokaci.

Kara karanta wannan

Bayan Doke Yari, Sanata Akpabio Ya Karɓi Rantsuwa, Ya Kama Aiki Matsayin Shugaban Majalisar Dattawa

Amincewa da kasafin kuɗi, ba tare da kuɗi ba

Sabon shugaban ya kuma buƙaci gwamnatin da kada ta riƙa tura kasafin kuɗi ba tare da cewa akwai kuɗaɗen a ƙasa zuwa Majalisar Dattawan ta 10 ba.

Ya bayyana cewa amincewa da kasafin kuɗi ba tare da kuɗaɗe a ƙasa ba, shi ne ainihin dalilin da yasa ake watsi da wasu ayyukan, kuma Majalisar Dattawa ta 10 za ta so haɗa kai da shugaban ƙasa wajen kawo ƙarshen wannan matsalar.

Abubuwan da suka taimaki Tajuddeen ya lashe zaɓen Majalisar Wakilai ta 10

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa a baya, kun karanta dalilai 7 da suka taimakawa sabon shugaban Majalisar Wakilan Najeriya, Tajuddeen Abbas wajen lashe zaɓen da ya gudana yau Talata.

Tajuddeen dai ya kasance ɗan takarar da jam'iyyar APC mai mulki ta tsaida a matsayin wanda take so ya shugabanci majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng