Sabon Ɗan Majalisa Ya Lashe Zaben Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Filato
- Sabon ɗan majalisa ya samu nasarar zama kakakin majalisar dokokin jihar Filato ranar Talata 13 ga watan Yuni, 2023
- Honorabul Moses Sule, mai wakiltar mazaɓar Mikang a majalisa ta 10 ya taɓa rike shugaban ƙaramar hukuma a jihar gabanin zama mamban majalisa
- Bayan haka majalisar ta zabi mataimakin kakakin majalisa, sannan sabon kakaki ya bai wa sauran mambobi rantsuwar kama aiki
Plateau - Majalisar dokokin jihar Filato ta zaɓi Honorabul Moses Sule a matsayin sabon kakakin majalisa ta 10 wacce ta fara aiki ranar Talata, 13 ga watan Yuni, 2023.
Channels tv ta tattaro cewa Sule ya kasance sabon ɗan majalisa kuma wannan ne karon farko da ya shiga zauren majalisar jihar Filato a matsayin wakilin mazaɓar Mikang.
Haka nan kuma majalisar da zaɓi mamba mai wakiltar mazaɓar Jos ta kudu, Honorabul Fom Gwottson, a matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar, kamar yadda Tribune ta rahoto.
Sanata Barau Jibrin: Muhimman Abubuwan Sani 5 Dangane Da Sabon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa
Bayan kammala zaben ne, magatakardan majalisar ya rantsar da sabon shugaban majalisar a bikin rantsuwar kama aiki wanda ya gudana yau Talata a Jos, babban birnin jiha.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sabon kakaki ya fara aiki nan take
Jim kaɗan bayan karɓan rantsuwar kama aiki, sabon kakakin majalisar ya rantsar da baki ɗaya takwarorinsa mambobin majalisar dokoki ta 10 a jihar Filato.
Legit.ng Hausa ta gano cewa majalisar dokokin jihar Filato ta ƙunshi mambobi 24 daga mazaɓu daban-daban na jihar. Jam'iyyar PDP mai mulki na da 16, APC na da 7 yayin da jam'iyyar YPP ke da guda ɗaya.
Idan baku manta ba a ranar 18 ga watan Maris, 2023, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta gudanar da zaɓen gwamna da mambobin majalisun jihohi 28.
A jihar Filato, jam'iyyar APC mai mulki ta sha mamaki, yayin da ta rasa kujerar gwamna kuma ta rasa mafi yawan kujerun majalisar dokokin jihar da ke Arewa ta Tsakiya.
Gwamna APC Ba Shi Da Lafiya, Ya Miƙa Mulki Ga Mataimakinsa
A wani rahoton na daban kuma Gwamnan jihar Ondo ya ɗauki hutu kana ya wuce zuwa ƙasar waje domin jinyar rashin lafiyar da take damunsa.
Wannan na ƙunshe ne a wata wasiƙa da mai girma gwamnan ya aike wa majalisar dokokin jihar ranar Talata 13 ga watan Yuni, 2023.
Asali: Legit.ng