Yanzu: Zababbun Yan Majalisa Sun Iso Da Wuri Don Kaddamar Da Majalisa Ta 10
- Zabbabun yan majalisun tarayya sun isa da wuri zuwa harabar Majalisun Tarayya da ke Abuja don kaddamar da Majalisa ta 10
- A bikin kaddamar da majalisar, zababbun yan majalisar zasu kuma su zabi wanda zasu jagoranci majalisun tarayya biyu
- An bayyana cewa yan majalisar sun isa harabar ginin da misalin karfe 6:30 na safiya
FCT, Abuja - Rahotanni da ke fitowa sun bayyana cewa yan majalisu sun isa harabar ginin majalisa da wuri a shirye-shiryen zaben shugabanni da kaddamar da majalisa ta 10.
Kamar yadda rahoton Nigerian Tribune ya shaida, yan majalisun sun isa harabar da misalin 6:30 na safiyar Talata, 13 ga Yuni.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An mamaye gaba daya harabar wajen da tarin jami'an tsaro a ciki da wajen ginin majalisar.
Wani shaidar gani da ido ya tabbatar cewa an rako yan majalisun cikin wasu manyan bas kirar coaster ta kofar fadar shugaban kasa wato Villa. A daya bangaren, wasu sun shigo harabar ta kofar SGF tare da rakiyar jami'an tsaro.
Kafin kaddamarwar, zabbabun yan majalisun za su gudanar da zabe don samar da shugabancin da zai ja ragamar majalisun tsahon shekara hudu.
Wannan zaben zai gudana a majalisar dattawa da majalisar wakilai na tarayyar kasar nan.
Su waye ke neman shugabancin?
Manyan mukaman da za zaba sune shugaban Majalisar Dattawa da kuma Kakakin Majalisar Wakilai.
Sanata Godswill Akpabio, Sanata Abdulaziz Yari da Sanata Orji Kalu sune ke kan gaba wajen neman shugabancin majalisar dattawa.
Sai dai, Sanata Akpabio ne ke da yiwuwar lashe zaben shugaban majalisar dattawan kasancewar shi ne wanda jam'iyyar APC da kuma Shugaba Bola Tinubu suka tsayar a matsayin dan takara.
Haka nan, a zauren majalisar wakilai akwai masu neman shugabancin majalisar. Amma, a yadda abin ya ke, Honarabul Abass Tajudeen shi ne yafi yiwuwar lashe kujerar bayan samun goyon bayan Shugaban Kasa Tinubu da kuma jam'iyyar APC.
Bola Tinubu: Yaushe yan Najeriya za su sa ran ganin sabbin ministoci?
A wani rahoton, Shugaba Bola Tinubu, bayan kama aiki ranar 29 ga watan Mayu, ya kara sanya sabon tsammani a zukatan yan Najeriya bayan wasu matakai da ya dauka.
Matakan shugaban kasar ya sanya yan Najeriya da dama jiran sunayen ministocinsa.
Sai dai, yan Najeriya na iya ganin sunan ministocin Tinubu daga 13 ga Yuni, bayan kaddamar da majalisun, da kuma 28 ga watan Yuni, lokacin da shugaban zai cika kwana sittin a kan karaga
Asali: Legit.ng