Sanata Akpabio Ne Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa, Uzodinma
- Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya nuna kwarin guiwar cewa Sanata Akpabio zai samu nasarar zama shugaban majalisar dattawa
- Ya ce kwamitin da shugaba Tinubu ya kirkira da nufin kawo karshen ruɗanin da ke tattara da tseren kujerar ya cimma nasara
- A cewarsa Sanata Ahmad Lawan zai yi duk mai yuwuwa wajen tabbatar da nasarar Akpabio gobe Talata
Abuja - Jam'iyyar All progressives Congress (APC) mai mulkin Najeriya ta jaddada kwarin guiwar cewa ɗan takarar da take goyon baya, Sanata Godswill Akpabio, ne zai lashe zaɓen shugaban majalisar dattawa.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa wannan na zuwa ne ƙasa da awanni 24 gabannin rantsar da majalisar dattawa ta 10, wanda zai gudana ranar Talata, 23 ga watan Yuni, 2023.
Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, wanda ba'a jima ba ya zama shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, shi ne ya bayyana yakinin jam'iyyarsa yayin hira da 'yan jarida a fadar shugaban ƙasa.
Uzodinma ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan ganawa da shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a fadarsa Aso Rock da ke Abuja ranar Litinin, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce kwamitin da shugaba Tinubu ya kafa kuma ya ɗora masa nauyin warware ruɗanin da ke tattare da tseren neman kujerun shugabancin majalisar dattawa ya samu nasararori.
A cewar gwamnan, kwamitin ya samu ci gaba a kokarinsa na haɗa kan Sanatoci da taimakon shugaban majalisar dattawa mai barin gado, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan.
Gwamna Uzodinma ya ƙara da cewa Sanata Lawan zai yi duk mai yuwuwa domin tabbatar da ɗan takarar da jam'iyyar ke goyon baya ya zama magajinsa a majalisar dattawa.
Da yake nasa jawabin, Akpabio, tsohon gwamnan jihar Anambra kuma tsohon Minista a gwamnatin Muhammadu Buhari, ya tabbatar da cewa majalisa ta 10 karƙashin jagorancinsa zata yi aiki cikin haɗin kai.
Ranar Dimokuradiyya: Dalilai 5 Da Suka Sa Ranar 12 Ga Watan Yuni Ke Da Muhimmanci A Tarihin Najeriya
Shugaba Tinubu Ya Rattaɓa Hannu Kan Dokar Bai Wa Dalibai Bashi
A wani rahoton na daban kuma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanya hannu kan kudirin dokar bai wa ɗaliban Najeriya bashi.
Wannan kudiri da shugaban kasa ya amince kuma ya sanya hannu zai ba ɗaliban Najeriya damar samun bashin gwamnati, wanda ba bu kuɗin ruwa a ciki.
Asali: Legit.ng