Gwamnan Katsina Ya Soke Filayen da Aka Raba Wa Wasu Mutane a Katsina
- Gwamnan Ƙatsina, Malam Dikko Radda, ya soke filayen da wasu jami'an gwamnati suka raba wa mutane
- A wata sanarwa daga ofishin shugaban ma'aikata, sabon gwamnan Katsina ya ce ba'a bi doka wajen raba filayen ba
- Dikko Radda na jam'iyyar APC ya gaji tsohon gwamna Aminu Bello Masari, wanda jam'iyyarsu ɗaya
Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya soke filayen da tsohuwar gwamnati karkashin Aminu Bello Masari ta raba wa mutane a faɗin jihar.
Leadership ta rahoto cewa wannan mataki na ƙunshe a wata sanarwa da daraktan sashin albarkatun ƙasa na ofishin shugaban ma'aikatan Katsina, Ado Yahaya, ya fitar.
Ya ce gwamna ya nuna takaicinsa da rashin jin daɗi kan yadda wasu shugabannin ma'aikatu a jihar suka raba filayen ba ta hanyar da doka ta tanada ba.
Ranar Dimokuradiyya: Dalilai 5 Da Suka Sa Ranar 12 Ga Watan Yuni Ke Da Muhimmanci A Tarihin Najeriya
A cewar Malam Raɗɗa, ya zama tilas ya dakatar da lamarin domin gwamnatin jiha ta hannun ma'aikatar kula da filayen ƙasa ne kaɗai ke da haƙƙin mallaka wa wani filo komi ƙanƙantarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Bugu da ƙari, duk wasu filaye da aka mallaka wa mutane ba tare da bin ƙa'idoji da tanadin doka ba, an soke su daga yanzu."
"Haka nan kuma duk wani jami'in gwamnati da aka gano da hannunsa a rabon waɗannan filaye ba bisa ƙa'ida ba zai fuskanci hukunci daidai da abinda ya aikata na saɓa doka," inji shi.
Gwamna Malam Dikko ya ɗauki wannan mataki ne kusan makonni biyu bayan ya karɓi rantsuwar kama aiki a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan Katsina ranar 29 ga watan Mayu.
Raɗɗa, wanda ya lashe zaben 18 ga watan Maris, da kuri'u masu rinjaye ya gaji tsohon gwamna, Aminu Bello Masari, na jam'iyyar APC mai mulki.
Legit.ng Hausa ta tuntuɓi ɗaya daga cikin waɗanda wannan matakin ya shafa a Katsina kuma ya ce gaskiya ba su ji daɗi ba amma suna fatan hakan ya kawo wani ci gaban.
Mutumin mai suna, Malam Yusuf, ya shaida wa wakilinmu cewa tabbas ya samu labari a aikace domin an ba shi wani babban fili a wajen gari yana noma amma bana an ce su dakata.
A kalamansa ya ce:
"Eh ni kam na samu labari saboda akwai wani fili da aka bani a wajen gari, labi ne, na sha wahala na gyara shi ya zama gona bara, har takin gida na kai bana amma yanzu an ce mana mu ɗan dakata."
"Idan har ana nufin an kwace gaskiya ba zan ji daɗi ba, na kashe kuɗi sosai a wurin bara da nufin zuwa bana zan amfana sosai duk da banu kaɗai bane. Ina fatan hakan ya zame wa jiharmu alheri."
"Ba Daina Zuwa Wurin Shugaba Tinubu Ba Saboda Abu 1" Gwamnan PDP da Yaje Villa Sau 4 a Sati Ya Faɗi Dalili
A Karon Farko a Tarihin Jihar Ebonyi, Gwamna Ya Nada Mace a Matsayin SSG
A wani labarin kuma Gwamnan jihar Ebonyi na APC ya kafa tarihi kwanaki kaɗan bayan karban mulki ranar 29 ga watan Mayun da ya shige.
Gwamna Nwifuru, ya naɗa Farfesa Grace Umezurike a matsayin Sakatariyar gwamnatin jiha (SSG) karo na farko a tarihin jihar Ebonyi da ke Kudu maso Gabas.
Asali: Legit.ng