Yarjejeniyar Da Aka Cimma Tsakanin Shugaba Tinubu Da Akpabio Kan Shugabancin Majalisar Dattawa

Yarjejeniyar Da Aka Cimma Tsakanin Shugaba Tinubu Da Akpabio Kan Shugabancin Majalisar Dattawa

  • Daga ƙarshe an bayyana yarjejeniyar da Tinubu da Akpabio suka cimmawa kan shugabancin majalisar dattawa ta 10
  • Shugaba Tinubu ya nemi Akpabio ya janye masa takara a lokacin zaɓen fidda gwanin shugaban ƙasa na jam'iyyar APC
  • A yarjejeniyar da suka cimma a tsakaninsu, idan Akpabio ya yi hakan Tinubu zai shige masa gaba ya zama shugaban majalisar dattawa

Abuja - Bayanai suna ta fitowa kan yadda shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya goyi bayan tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Sanata godswill Akpabio, ya zaman shugaban majalisar dattawa ta 10.

Majiyoyi na kusa da shugaban ƙasan sun gayawa jaridar Punch a ranar Asabar, cewa yarjejeniyar sanya Akpabio ya zama shugaban majalisar dattawa an cimmata ne ana saura kwana ɗaya ayi zaɓen fidda gwanin zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Shettima da Matar Shugaban Kasa Sun Halarci Zaman Bankwana Na Majalisar Dattawa, Sun Ja Hankali

Yarjejeniyar Tinubu da Akpabio kan shugabancin majalisa
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Punch.com
Asali: Facebook

Majiyar ta bayyana cewa Tinubu ya gana da Akpabio ana saura ɗaya a gudanar da zaɓen fidda gwanin shugaban ƙasa na APC, inda ya buƙace shi da ya janye masa takara.

Tinubu gaya masa cewa idan ya amince da hakan, takarar Tinubu za ta ƙara samun tagomashi saboda shi za a fara kira domin ya yi magana.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sharaɗin Akpabio kafin ya janye

A cewar majiyar wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda baya da hurumin yin magana akan lamarin, ya bayyana cewa Akpabio ya amince da hakan amma ya buƙaci sanin wane amfani zai samu saboda ya yi murabus daga minista kuma baya takarar sanata.

Tinubu ya ba shi tabbacin cewa za a saka masa da kujerar shugaban majalisar dattawa saboda sadaukarwar da zai yi ya janye masa takara.

“Asiwaju (Tinubu) ya tabbatar masa da cewa za a mara masa baya ya zama shugaban majalisar dattawa. A haka aka cimma wannan yarjejeniyar." A cewar majiyar

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Bayyana Abin Da Ya Tattauna Da Sarakunan Gargajiya, Ya Nemi Alfarma 1 Daga Gare Su

PDP Ta Bayyana Zabin Yan Majalisunta a Shugabancin Majalisa

A wani rahoton na daban kuma, jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), ta faɗi ƴan takarar da ƴan majalisunta za su zaɓa a shugabancin majalisa ta 10.

PDP tace ƴan majalisunta na da ƴancin zaɓar duk waɗanda suka kwanta musu a rai domin ba za ta yi musu katsalandan a zaɓinsu ba.

Jam'iyyar tace ta cimma matsaya kan shugabancin majalisar amma ta bar wa kanta sani kawai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng