Tinubu Ya Bayyana Abin Da Ya Tattauna Da Sarakunan Gargajiya, Ya Nemi Alfarma 1 Daga Gare Su

Tinubu Ya Bayyana Abin Da Ya Tattauna Da Sarakunan Gargajiya, Ya Nemi Alfarma 1 Daga Gare Su

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci sarakunan gargajiya su goyi bayan manufofin gwamnatinsa
  • Ya yi wannan kiran ne ranar Juma’a, 9 ga watan Yuni, a yayin wata ganawa da ya yi da sarakunan gargajiya a fadarsa da ke Abuja
  • Shugaba Tinubu ya kuma ba su tabbacin cewa za su samu goyon bayan gwamnatinsa domin su yi ayyukansu yadda ya kamata

FCT, Aso Villa - Sakamakon ganawar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi da sarakunan gargajiyan Najeriya ya bayyana.

Shugaba Tinubu, ta wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Juma’a, 9 ga watan Yuni, ya bayyana cewa ganawarsa da sarakunan ta yi kyau, inda ya bayyana cewa ya samu kyakkyawar alaƙa da su a yayin ganawar.

Tinubu ya gana da sarakunan gargajiya
Tinubu ya nemi sarakunan gargajiya su bai wa gwamnatinsa hadin kai. Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Tinubu ya nemi sarakunan su marawa gwamnatinsa baya

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Yi Magana Kan Kujerar Ministan da Aka Masa Tayi Bayan Ganawa da Shugaba Tinubu

Tinubu ya buƙaci masu rike da sarautun na gargajiya, da su haɗa ƙarfi da ƙarfe su mara wa gwamnatinsa da manufofinsa ga 'yan ƙasa baya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Tinubu a shafinsa na Tuwita:

"Na ji daɗin zama na, a safiyar yau, da taron sarakunan gargajiya daga sassa daban-daban na ƙasar nan."
“A yayin tattaunawar mu, na ba su aikin tallafawa ƙoƙarin da gwamnati ke yi na samun dawwamammen zaman lafiya da haɗin kai ta hanyar ɗabbaƙa halayen kirki da kishin ƙasa."

Tinubu ya ɗaukarwa sarakunan alƙawari

Shugaba Tinubu ya kuma ba su tabbacin cewa, zai ba su dukkanin goyon bayan da suke buƙata don gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, a matsayinsu na jakadun al’adun Najeriya.

Taron dai na daga cikin jerin abubuwan da shugaban ya yi da masu ruwa da tsaki tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana da Manyan Sarakunan Kasar Nan a Villa, Sarkin Musulmi Ya Faɗi Wasu Kalamai

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'adu Abubakar, Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero Obi na Onitsha, Alfred Achebe, Oba Elegushi, Alayeluwa Saheed Ademola da ƙarin wasu da dama.

Tinubu yayi wata muhimmiyar ganawa da Kwankwaso a Aso Rock

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa a baya, Shugaba Bola Tinubu ya yi wata muhimmiyar ganawa da ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Wannan dai shi ne karo na biyu da shugabannin biyu suka gana, bayan wacce suka yi birnin Paris na ƙasar Faransa a lokacin da ake shirye-shiryen rantsar da shugaban ƙasar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an tsinkayi Kwankwaso a fadar Shugaba Tinubu, ranar Juma’a 9 ga watan Yuni, da misalin karfe 5:30 na yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Online view pixel