“Zaman Lafiyar Najeriya Ya Fi Aljihunmu Muhimmanci”, Shettima Ga Zababbun Sanatoci

“Zaman Lafiyar Najeriya Ya Fi Aljihunmu Muhimmanci”, Shettima Ga Zababbun Sanatoci

  • Mataimakin shugaban kasa ya shawarci zababbun sanatoci da kada su karbi cin hanci daga masu neman takarar shugabancin majalisar dattawa
  • Kashim Shettima ya bayyana cewa daidaituwar Najeriya shine abun da ya kamata yan majalisar su sanya a gaba ba wai aljihunsu ba
  • A ranar Talata, 13 ga watan Yuni ne za a rantsar da majalisar dokokin tarayya ta 10 tare da zaben shugabanninsu

Abuja - Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bukaci zababbun sanatoci da su yi zabe da hankali idan aka rantsar da zauren majalisar dattawa a mako mai zuwa.

Majalisar dattawa za ta zabi shugabanninta na majalisa ta 10 a ranar Talata, 13 ga watan Yuni.

Kashim Shettima
“Zaman Lafiyar Najeriya Ya Fi Aljihunmu Muhimmanci”, Shettima Ga Zababbun Sanatoci Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Da yake magana yayin zaman rufe majalisar dattawa ta tara a ranar Asabar, 10 ga watan Yuni, Shettima ya fada ma yan majalisar cewa zaman lafiyan kasar ya fi cika aljihunsu daraja, jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

"Za Ka Koya Mun Yadda Ake Komawa Majalisa Ba Tare Da Zaben Fidda Gwani Ba", Okorocha Ya Yi Shagube Ga Lawan

Ana ta zarge-zargen cewa wasu masu neman takarar shugaban majalisar dattawan na amfani da kudi wajen siye zababbun sanatoci domin su zabe su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Koda dai jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta tsayar da Godswill Akpabio, tsohon ministan harkokin Neja Delta, a matsayin zabinta na wanda zai zama shugaban majalisar dattawan, Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan Zamfara da Orji Uzor Kalu, sun ki janyewa daga takarar.

Ra'ayin kasa ya kamata ku duba wajen zabar shugabanni ba aljihunku ba, Shettima ga zababbun sanatoci

Mataimakin shugaban kasar ya ce ra'ayin kasar shine abun da ya kamata su duba wajen zabar wanda zai zama shugaban majalisar dattawan da mataimakinsa, rahoton Punch.

Ya ce:

"Ga takwarorina masu jiran gado, na barku da wani dan misali, 'zaman lafiyar kasar nan, ya fi daidaituwar aljihunmu'. A ranar Talata, mu yi zabe da hankali, mu zabe don kasar Najeriya."

Kara karanta wannan

Shettima da Matar Shugaban Kasa Sun Halarci Zaman Bankwana Na Majalisar Dattawa, Sun Ja Hankali

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana takwarorinsa a matsayin "abokai wadanda suka zama masu muhimmanci a bangaren tarihina.

"Mun yi aiki kafada da kafada a lokacin da ake fuskantar matsaloli kuma mun yi aiki tukuru domin ci gaban al’ummarmu."

Shugaban majalisar dattawa: Zababbun Sanatoci za su siyar da kuri'unsu $5,000, $10,000 ko fiye da haka

A wani labarin, mun ji cewa yayin da ake shirye-shiryen rantsar da majalisar dokokin tarayya ta 10 a ranar Talata, 13 ga watan Yuni, bayanai sun nuna zababbun sanatoci na kokarin siyar da kuri'unsu ga masu neman takarar shugabancin majalisar.

A majalisar dattawa, yan takara sun fara kokarin zawarcin yan majalisa don marawa kudirinsu na son darewa kujerar shugaban majalisar dattawan baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng