Wike Ya Yaba Wa Shugaban Kasa Tinubu Bisa Dakatar da Gwamnan CBN

Wike Ya Yaba Wa Shugaban Kasa Tinubu Bisa Dakatar da Gwamnan CBN

  • Nyesom Wike, jagoran tawagar G-5 da ta ƙunshi gwamnonin PDP, ya yaba wa shugaba Tinubu bisa dakatar da Emefiele
  • Tsohon gwamnan jihar Ribas na ɗaya daga cikin masu sukar tsarukan da gwamnan CBN ya kawo musamman canjin kuɗi
  • Haka nan kuma Wike ya jinjina wa Tinubu bisa rattaɓa hannu kan dokar ritaya da fansho ga ma'aikatan sashin shari'a

Tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya jinjina wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, kan matakin da ya ɗauka na dakatar da Godwin Emefiele daga matsayin gwamnan babban banki (CBN)

Channels tv ta tattaro cewa Tinubu ya dakatar da Emefiele ranar Jumu'a da yamma kuma ya umarce shi da ya gaggauta mika mulki ga mataimakin gwamna na sashin ayyuka, Folashodun Shonubi.

Tinubu da Wike.
Wike Ya Yaba Wa Shugaban Kasa Tinubu Bisa Dakatar da Gwamnan CBN Hoto: Bola Tinubu
Asali: Twitter

Da yake martani kan wannan ci gaban, Wike ya ayyana matakin da shugaban ƙasa ya ɗauka kan Emefiele a matsayin babban kuma a lokacin da ya dace.

Kara karanta wannan

Godwin Emefiele: Wike Ya Yi Martani Ga Hukuncin Tinubu Na Dakatar Da Gwamnan CBN

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa Wike, a lokacin yana kan kujerar gwamna, yana cikin manyan masu sukar tsare-tsaren da Emefiele ya ɓullo da su, musamman sauya fasalin takardun kuɗi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban Tinubu ya yi abinda ya dace a bangaren shari'a - Wike

Bugu da ƙari, tsohon gwamnan jihar Ribas, ya ƙara yaba wa shugaba Tinubu bisa amince wa da adadin shekarun ritaya da kuma fansho ga ma'aikatan bangaren shari'a.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, Wike ya ce abinda shugaban ƙasa Tinubu ya yi zai ƙara samar da natsuwa da haɓaka ɓangaren shari'a a ƙasar nan.

Ya ƙara da bayanin cewa shi da sauran mambibin tawagar G-5 sun ji daɗin yadda shugaban kasan ya fara tafiyar da mulkinsa abin misali kuma ya maida hankali don ganin Najeriya ta dawo kan ganiyarta.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Yi Magana Kan Kujerar Ministan da Aka Masa Tayi Bayan Ganawa da Shugaba Tinubu

Idan baku manta ba, Wike da sauran 'yan tawagarsa sun gana da shugaban kasa Tinubu a Villa, inda suka faɗa masa abinda suka kafu a kai da kuma halin da ƙasa ke ciki.

Kwankwaso Ya Yi Karin Haske Kan Tayin da Shugaba Tinubu Ya Masa Na Minista

A wani rahoton na daban Kwankwaso ya yi karin bayani kan kujerar Minista da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya masa ta yi a gwamnatinsa.

Jim kaɗan bayan ganawa da Tinubu, tsohon gwamnan Kano ya ce sun tattauna batutuwa da dama ciki harda zancen naɗa shi a matsayin Minista.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262