"Ba Zan Daina Ziyartar Shugaban Kasa Tinubu Ba" Gwamna Makinde
- Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ce ba zai daina kai ziyara fadar shugaban kasa ba har sai ya samu abinda yake zuwa nema
- Kusan sau huɗu gwamnan ya ziyarci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, tun bayan rantsuwar kama aiki ranar 29 ga watan Mayu
- A cewarsa yana zuwa ganin Tinubu ne domin gwamnatin tarayya ta maida wa Oyo kuɗin ayyukan titunan da ta gudanar
Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ce ba zai daina kai ziyara ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ba ko me mutane zasu faɗa, kamar yadda The Nation ta rahoto.
Gwamna Makinde, mamban tawagar G-5 a jam'iyyar PDP, ya bayyana haka ne a wurin kaddamar da fara aikin faɗaɗa titin Akobo, Ojurin/Odogbo Barracks, Olorunda Abas Junction.
Jaridar Vanguard ta tattaro Makinde na cewa:
"Yayin da nake zuwa Abuja domin gana wa da shugaban ƙasa, na san wasu na nan sun fara yaɗa maganganu cewa tun da aka rantsar da shugaban ƙasa na je Aso Rock kusan sau huɗu a mako ɗaya."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Ina kuke so na je? Ko burinku na wanke ƙafa na tafi Yola? Don haka duk abinda zaku faɗa ba zai maƙale mun ba zan ci gaba da zuwa wurin da ake da ikon maido wa jihar Oyo kuɗin da ta kashe a titunan gwamnatin tarayya."
"Saboda haka zan ci gaba zagarabtu a fadar shugaban kasa ina rokon a dawo mana da kuɗin. Kaima shugaban ƙaramar hukumar Lagelu, da zaran na karɓo kuɗin daga FG ka zo wajena ka karɓi naku."
Wannan kalaman gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece kuce da sukar yawan zuwansa wurin shugaban ƙasa duk da ba jam'iyyarsu ɗaya ba.
Amma Makinde yace yana mamakin masu magana domin ina zai riƙa kai ziyara bayan ya san inda zai je idan Allah ya taimake shi a dawo masa da kuɗin.
Shugaba Tinubu Ya Gana da Manyan Sarakunan Kasar Nan a Villa, Bayanai Sun Fito
A wani rahoton kuma Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da Sarkin Musulmi, Sarkin Kano, Sarkin Zazzau da sauran sarakunan Najeriya a Villa.
Ana tsammanin Tinubu zai taɓo batun haɗa kan kasa da kuma tsamo Najeriya daga yanayin da take ciki a zamansa da Sarakunan.
Asali: Legit.ng