Yadda Hadin-kan da Majalisa ta ba Shugaba Buhari Ya Haifawa Najeriya Matsala - Sanata
- Muhammad Ali Ndume ya soki dangantakar da majalisa ta tara ta samu da Shugaba Muhammadu Buhari
- Sanatan jihar Borno ta Kudu ya ce ‘yan majalisa sun wuce gona da iri wajen hada-kai da Shugaban Najeriya
- A bangaren bashi, Ndume ya nuna ba ayi nazarin tasirin bashin da gwamnatin tarayya ta rika karbowa ba
Abuja - Muhammad Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa ya ce abokan aikinsa sun ba Muhammadu Buhari hadin-kai fiye da kima.
A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Sanata Muhammad Ali Ndume ya bayyana cewa akwai inda majalisa ta tara tayi abin a yaba, amma ba za a rasa gazawa ba.
Sanatan yake cewa akwai tsare-tsare da manufofin gwamnatin Buhari da ya kamata a ce ‘yan majalisar tarayya sun yi adawa da su, amma hakan ya gagara.
A cewarsa, hadin-kan da aka rika ba gwamnatin da ta wuce bai taimaki Najeriya ba, ba a nuna kishi ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Ba a taba yin majalisar da ta ba bangaren zartarwa hadin-kai kamar majalisar tarayya ta tara ba.
Duk da cewa ya kamata mu bada hadin-kai, amma abin ya yi yawa, kuma hakan ya zama matsala ga kasar nan musamman a bangaren bashin da aka karbo.
Ba mu yi bincike da kyau ba, kuma ba mu duba amfanin karbo bashin da aka ci a baya ba, a duba yadda za a biya kudin da abubuwan da suka biyo baya."
- Muhammad Ali Ndume
Yaki da rashin gaskiya
A game da yaki da cin hanci da rashawa, Daily Trust ta ce Sanata Ndume ya ce gwamnatin Buhari ba ta iya cika alkawarin da tayi wajen hawa mulki ba.
"Abin da mu ka yi alkawari a gwamnatin shi ne za mu yaki cin hanci da rashawa kai-tsaye, amma babu wata doka da aka yi a game da wannan.
Kamar yadda na fada, an samu hadin-kai da gwamnati, amma abin ya wuce gona da iri.”
- Muhammad Ali Ndume
Kudirin aikin Alkalai
Majalisa ta aika kudirin Aso Rock, amma har Muhammadu Buhari ya bar kan mulki bai tanka shi ba, sai a jiya aka ji labari kudirin ya zama doka a kasa.
Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu a kudirin aikin alkalanci, hakan ya nufin an canza shekarun ritayar Alkalai, kowanensu zai kai shekara 70 a kotu.
Asali: Legit.ng