Gwamnan Enugu Ya Gana da Shugaba Tinubu, Ya Nemi Ya Sako Nnamdi Kanu

Gwamnan Enugu Ya Gana da Shugaba Tinubu, Ya Nemi Ya Sako Nnamdi Kanu

  • Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya gana da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock da ke birnin tarayya Abuja
  • Da yake zantawa da yan jarida, Mbah, ya bayyana wasu daga cikin batutuwan da ya tattauna da shugaba Tinubu
  • Ya ce daga ciki, ya roki shugaban ya duba yuwuwar sako shugaban ƙungiyar yan aware da aka ayyana da ta yan ta'adda IPOB

FCT Abuja - Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu ya fara tattauna wa da shugaban kasa a kokarinsa na ganin an sako wanda ya yi ikirarin zama shugaban ƙungiyar 'yan aware (IPOB).

Yayin ganawa da shugaban Najeriya, Bola Tinubu, gwamna Mbah ya roƙi ya duba yuwuwar sako Kanu, shugaban IPOB, wacce aka ayyana a matsayin ƙungiyar 'yan ta'adda, Channels tv ta rahoto.

Gwamna Mbah da Kanu.
Gwamnan Enugu Ya Gana da Shugaba Tinubu, Ya Nemi Ya Sako Nnamdi Kanu Hoto: channelstv
Asali: UGC

Gwamna Mbah ya faɗa wa yan jaridan gidan gwamnati cewa yayin ganawa da Tinubu ranar Alhamis, daga cikin batutuwan da suka tattauna harda rokon sakin Kanu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Muhimman Kalaman da Gwamnonin G5 Suka Faɗa Wa Shugaba Tinubu Sun Bayyana

Idan baku manta ba, shugaban ƙungiyar masu fafutukar ɓallewa daga Najeriya su kafa ƙasar Biafara, Kanu, na fuskantar shari'a gaban Kotu kan tuhume-tuhume da dama.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma a cewar gwamnan jihar Enugu da ke Kudu maso Gabashin Najeriya, sako Kanu zai ƙara ɗaga yunkurin ceto ƙasar nan, wanda shugaba Tinubu ya fara tun da ya hau mulki.

Daily Trust ta rahoto Gwamna na cewa:

"Mun tattauna kan batun sako Nnamdi Kanu, kun sani cewa shiyyar Kudu Maso Gabas ta haɗa kai ta roki a sako Kanu tun ba yau ba. Mun duba wannan kuma mun roki shugaban kasa."

Shin Tinubu zai amince da buƙatar sakin Nnamdi Kanu?

Gwamna Peter Mbah, ya bayyana kwarin guiwa da fatan cewa shugaban ƙasa zai duba wannan buƙata da idon basira da kuma alfarma.

Ya kuma ƙara da bayanin cewa, yayin wannan taro, ya roki gwamnatin tarayya ta taimaka wajen zakulo albarkatun ƙasa da aka yi watsi da su a jihar Enugu domin mutane su amfana.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Tinubu Ya Gana da Gwamnonin G5 Kan Wani Muhimmin Abu, Bayanai Sun Fito

Gwamna Makinde Ya Fadi Abinda Tawagar G5 Ta Tattauna da Shugaba Tinubu

A wani rahoton na daban kuma Gwamnan Oyo kuma mamban tawagar G-5 ya faɗi batutuwan da suka tattauna a wurin ganawa da shugaba Tinubu.

A ranar Alhamis, 8 ga watan Yuni, 2023, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da gwamnonin G-5 na PDP a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262